Home Back

Gwamnatin Kano za ta shirya gagarumin taron horaswa kan sana’o’in dogaro da kai da raba jari

premiumtimesng.com 2024/7/3
ABBA YA TADA KANAWA TSAYE: Ya kafa Kwamitocin Binciken Yadda aka Sayar da Kadarorin Gwamnati da Rigingimun Siyasa tsakanin 2015 – 2023

Babban Mai Taimakawa na Gwamnan Jihar Kano na Musamman kan Harkokin Sana’o’in Dogaro da kai, Abdulmumin Tijjani, ya bayyana cewa Gwamnatin Abba Kabir-Yusif za ta shirya gagarimin taron horaswa kan sana’o’in dogaro da kai.

Tijjani wanda aka fi sani da Mai POS, ya
bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai da ke aiki a ofishin Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam.

Tijjani Mai POS ya yi bayanin cewa shirin zai ƙunshi bayar da cikakken jarin sana’o’in dogaro da kai ga matasa, bayan an ba su horo na musamman a kan wannan fanni, tare da karrama wasu daga cikin mashahuran mutanen da suka yi fice a fannin sana’o’in dogaro da kai a jihar.

Abdulmumin Tijjani wanda shi ne tsohon ɗan takarar majalisar tarayya na ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa, ya ƙara da cewa sauran abubuwan da taron zai ƙunsa Sun haɗar da gayyatar kamfanoni masu zaman kan su tare da bayar kyautuka ga ɗaliban makarantun da suka yi fice wajen koyar da sana’o’in dogaro da kai, bayan nuna bajintar su a yayin taron.

Babban Mai Taimaka wa Gwamnan na Musamman ya ce, “gagarumin shirin bayar da horon ya
haɗa matasa maza da mata da manya da ma M
masu buƙata ta musamman.

Daga ƙarshe ya miƙa saƙon sa na Sallah da murnar cika shekara guda ga Gwamna Abba Kabir-Yusuf da Mataimakin sa Aminu Abdussalam da kuma jagoran Kwankwasiyya,

Sanata Rabi’u Kwankwaso da al’ummar ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa da ma Jihar Kano baki ɗaya.

People are also reading