Home Back

HARAJIN TSARON INTANET: Kwamitin Majalisar Dattawa ya ce Harajin kashi 0.5 na ‘Cybersecurity Levy’ ba shi da illa ga ‘yan Najeriya

premiumtimesng.com 2024/6/16
Daga yanzu duk mai watsa labarai a Najeriya ta yanar gizo ko Soshiyal Midiya sai yayi rajista da NBC

Shugaban Kwamitin Tsaron Ƙasa da Leƙen Asiri, Sanata Shehu Buba, ya bayyana cewa ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya biyan kashi 0.5 na kowace tiransifa da suka yi daga asusun bankunan su, ba a ƙirƙiro shi ba don a zafafa wa mutane, sai don a ƙara samar da tsaro a cikin ƙasa, tare kuma da kare tattalin arzikin ƙasar.

Buba, Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, ya bayyana haka ne a ranar Alhamis.

Tuni dai ‘yan Najeriya da dama ke ci gaba da nuna rashin amincewa da sabon tsarin, wanda zai fara aiki kafin ƙarshen watan Mayu.

Sai dai kuma Majalisar Tarayya ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) cewa kada ya fara sa a cire kuɗaɗen.

Umarnin ya biyo bayan wani roƙo ne da Shugaban Marasa Rinjaye, Kingsley Chinda ya yi.

To sai dai kuma Sanata Buba ya ce za a ƙaƙaba harajin domin kare ‘yan Najeriya , musamman talakawa da marasa galihu.

Buba ya ce sai da Majalisar Dattawa da ta Tarayya suka amince kafin Shugaban Ƙasa ya sa wa ƙudirin hannu ya zama doka.

“Kuma maganar gaskiya tun a cikin 2015 ya kamata a fara amfani da wannan haraji, amma sai aka yi jinkiri, sanadiyyar wata irin fassara da aka yi wa tsarin da kuma wasu bayanan da ba a fayyace dalla-dalla a cikin tsarin ba.”

Tuni dai har ƙungiyar SERAP, BudgiT da wasu mutum 38 suka maka Gwamnatin Tarayya kotu, su na so a hana CBN bai wa bankuna umarnin fara cirar kuɗaɗen da sunan haraji.

Idan ba a manya ba, cikin makon jiya ne SERAP ta yi kira ga Shugaba Tinubu, tare da yi masa gargaɗin cewa ”Kada ka bar Gwamnan CBN Cardoso ya ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya da harajin ‘Cybersecurity’.

Ƙungiyar Rajin Kare Haƙƙin Jama’a ta SERAP, ta yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu cewa , “ya yi amfani da ƙarfin ikon sa ya gaggauta taka wa Babban Bankin Najeriya (CBN) burki, kada ya bari bankuna su fara cirar Harajin Daƙile Harƙallar Kuɗaɗe ta Hanyar Intanet, wato ‘Cybersecurity’ da aka ƙaƙaba cikin wannan satin.

SERAP ta ce ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya biyan harajin ta hanyar cire masu harajin daga kuɗaɗen taransifa a bankuna, da Gwamnan CBN Yemi Cardoso zai fara, ya karya Dokar Najeriya ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Cikin wata sanarwar da suka fitar a ranar Talata, SERAP, wadda ƙungiya ce mai sa-ido kan batutuwan cin hanci da rashawa, ta yi kira da a sake duba dokar wadda CBN ke so ta yi amfani da ita wajen ƙaƙaba cire harajin.

“Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta umartar Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya gabatar da ƙudirin gyaran Sashe na 44 da sauran batutuwan da ke ƙarƙashin Dokar ‘Cybercrime’ Act ta 2024.”

Sun kuma yi kira ga Shugaba Tinubu ya dakatar da Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro (NSA) daga fara aiki da Sashe na 44 na Dokar ‘Cybercrime’ ta 2024.

Cikin sanarwar wadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya sa wa hannu, ya ce, “mun bai wa Shugaban Ƙasa wa’adin sa’o’i 48 ya hana CBN fara amfani da Dokar Cire Harajin Daƙile Harƙallar Kuɗaɗe ta Intanet, wadda za a ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya.”

Sun ce cirar kuɗaɗen haramun ne, kuma ya keta doka.

SERAP ta ce lauyan ta Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) ya fara shirye-shiryen garzayawa kotu domin shigar da ƙara, idan ba a soke cirar harajin ba.

A ranar Litinin ce dai CBN ya umarci bakuna cewa daga ranar 23 ga Mayu, 2024, su riƙa cirar kashi 0.5 na Harajin Daƙile Harƙallar Kuɗaɗe a Intanet, wato ‘Cybersecurity Levy’, daga asusun masu tura kuɗaɗe a banki.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin wani haraji da ya yi kama da harajin-jiki-magayi, wanda CBN ya umarci bankuna su riƙa cirar kashi 0.5 na Harajin Daƙile Harƙallar Kuɗaɗe a Intanet, daga asusun masu tura kuɗaɗe.

Daga ranar 23 ga Mayu, 2024, duk wani wanda ya tura kuɗaɗe ta hanyar amfani da waya, P.O.S, ATM da sauran hanyoyin hada-hadar tura kuɗaɗe na zamani, to za a riƙa cirar harajin kashi 0.5 da adadin kuɗaɗen da ya tura.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ya bada wannan umarni ga dukkan bankunan kasuwanci a ƙasar nan baki ɗaya.

Sanarwar da CBN ya fitar a ranar Litinin, na ɗauke da sanarwar cewa za a fara cirar waɗannan kuɗaɗen haraji daga nan da makonni biyu bayan fitar wannan sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa tunatarwa ce aka yi wa dukkan bankuna, domin tuni sun san akwai wannan batu a ƙasa kwance, tun ranar 5 ga Yuni, 2018 da aka aika masu da sanarwa mai lamba Ref: BPS/DIR/GEN/CIR/05/008 da kuma ta ranar 8 ga Oktoba, 2018 mai lamba Ref: BSD/DIR/GEN/LAB/11/023, bisa yadda za a bi umarnin Dokar Haramcin Harƙallar Kuɗaɗe ta Intanet da Na’urorin Zamani, ta 2015.

“Duk wanda aka cirar wa kuɗin za rubuta a rasiɗin cirar kuɗi cewa: “Cybersecurity Levy’ a kan sa.

Sanarwar ta ce za a ci tarar bankunan suka ƙi bin wannan umarnin za su fuskanci tara har ta kashi 2 bisa 100 na adadin yawan kuɗaɗen da aka yi hada-hadar na jimillar shekara ɗaya.

Cikin makon jiya ne dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da Ofishin NSA ya yi kira a riƙa tilasta bin dokar haramta hada-hadar kuɗaɗen harƙalla ta hanyar intanet a Najeriya.

Ofishin Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa (NSA), ya yi kira da a tilasta bin doka da odar da ke shimfiɗe a ƙarƙashin Dokar Haramcin Hada-hadar Kuɗaɗen Harƙalla ta Hanyar Intanet, dokar da aka fi sani da ‘cybercrime law’.

Ofishin NSA Nuhu Ribadu ya yi wannan kira a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, bayan wani ƙasaitaccen taron Manyan Jami’an Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙarƙashin Ƙasa a Afrika suka gudanar.

Taron dai kamar yadda sanarwar ta bayyana, an gudanar da shi ne a Abuja, tsakanin 22 zuwa 23 ga Afrilu.

Daga cikin manufofi da ƙudirorin da aka cimma bayan taron, sun haɗa da yin kira “a ƙara inganta hanyoyin yaƙi tare da daƙile ayyukan harƙallar kuɗaɗe ta hanyar intanet a Afrika.”

Ƙudirin ya kuma haɗa da yin kira ga gwamnatocin Afrika su “ƙirƙiro matakan hana amfani da soshiyal midiya da sauran kafafen da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen yaɗa mugayen manufofin su.”

Haka dai sanarwar wadda Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na Ofishin NSA, Zakari Mijinyawa ta ƙunsa.

Hanyoyin da ake so a daƙile amfani da su wajen aikata laifukan sun haɗa da wayoyin GSM, kamfanonin sadarwa na tarho, intanet, bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe, kamfanonin inshora da Cibiyar Hada-hadar Hannayen Jari.

Ofishin NSA ya yi kira a riƙa tilasta bin dokar haramta hada-hadar kuɗaɗen harƙalla ta hanyar intanet a Najeriya.

People are also reading