Home Back

Kamfanin Google Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Darasi 10 Kan Kirkirarriyar Basira

leadership.ng 2024/10/6
Kamfani

A wani yunƙurin magance yawan buƙatun da jama’a suke da su musamman masu kirkire-kirkire kan ilimin fasahar nan ta kirkirarriyar basira (AI) da ake ya yi a halin yanzu, Kamfanin Google ya ƙaddamar da shirin koyarwa kyauta a darussa daban-daban har guda 10 da nufin koyar da masu sha’awa abubuwa na ilimi da sanin muhimman batutuwan da suka shafi wannan muhimman basirar.

A daidai lokacin da fasahar AI ke kara kawo gagarumin sauyi da canji a masana’antu da duniyar fasahar kere-kere, Google ya yi shirin yadda masu baiwar kere-kere za su samu cin gajiyar ilimin AI da kuma zurfafa saninsu kan sabon basirar domin tafiya da zamani.

Sabon yunkurin Google kamar yadda jami’in kamfanin, Mirasys India ya bayyana, sun kunshi cikakkun darussa guda 10 da aka tsara da nufin bayar da asasi da ginshikin samun ilimi da fahimtar fasahar AI.
Kyauta ne kwas-kwasan a wani azama da Google ke yi wajen bunkasa ci gaba mai tasowa a duniyar kere-kere da kuma na fasaha.

Daga cikin darussan sun kunshi gabatar da mene ne ma kirkirarriniyar basirar, gabatarwa zuwa ga samfurin harsuna, gabatarwa kan nauyin AI, da dai sauran bangarorin da suka shafi yadda za a samu ilimi da kyakkyawar fahimta kan ilimin kirkirarriyar basira ta AI.

Wakilinmu ya labarto cewa tunin jama’a da dama musamman masu ilimi ko sha’awa a bangaren kere-kere suka dukufa wajen ganin sun samu damar cin wannan gajiyar ilimin musamman ganin yadda Google ya shelanta cewa kyauta ne samun wadannan ilimin.

People are also reading