Home Back

Bayan Sace Mutum 150, Ƴan Bindiga Sun Ƙara Yin Garkuwa da Mutane Sama da 50 a Arewa

legit.ng 2024/7/2
  • Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 56 a kauyuka biyu da ke yankin kananan hukumomin Munya da Tunga a jihar Neja
  • Shugaban ƙaramar hukumar Nunya, Alhaji Aminu Najume ya tabbatar da sace mutanen, inda ya ce maharan sun nemi kuɗin fansa
  • Wannan na zuwa ne kusan mako guda bayan ƴan bindiga sun ɗauke mutum 150 a kauyen Kuchi, sun nemi fansar N150m

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutum 30 a ƙauyen Kakuru da ke ƙaramar hukumar Munya a jihar Neja.

Har ila yau a wani harin na daban, ƴan bindiga sun sace mutane 26 daga ƙauyen Adogo Mallam, shi kuma a ƙaramar hukumar Tunga duk a jihar Neja.

Gwamna Umar Bago na jihar Niger.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 56 a kauyuka 2 a jihar Niger Hoto: Mohammed Umar Bago Asali: Twitter

Maharan sun aikata wannan ta'adi na garkuwa da mutane a ƙauyukan tsakanun ranar Lahadi zuwa Litinin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban karamar hukumar Munya, Alhaji Aminu Najume, ya tabbatar da sace karin mutane 30 a kauyen Kakuru, inda ya ce maharan sun nemi kuɗin fansa.

"Mutum biyu ne kawai suka sako su je su nemi kudi su biya a sako ‘yan uwansu. Sun sako wani mutum da aka yi garkuwa da shi tare da matarsa ​​da ‘ya’yansa uku don ya je ya tattaro kudin fansa."

Shugaban ƙaramar hukumar ya koka kan rashin tura jami'an tsaro yankin, wanda a yanzu mutane sun tashi daga gidajen su saboda rashin tsaro.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja ta kuma tabbatar da sace mutane 26 a yannin karamar hukumar Shiroro.

Ƙauyen Kakuru da aka sace mutane 30 na da tazarar kilomita biyar daga garin Kuchi inda ƴan bindiga suka sace mutane 150 a makon jiya.

‘Yan ta’addan da suka sace mutane 150 a Kuchi sun nemi a biya fansa N150m, watau N1m kan kowane mutum ɗaya, sun sanya wa'adin 15 ga watan Yuni.

Sun ce idan ba su biyan kuɗin ba za su riƙa kashe mutum biyar a kowace rana har zuwa lokacin da za su biya kuɗin fansar.

Yan bindiga sun kashe kansila

A wani rahoton kuma miyagun ƴan bindiga sun kashe kansila da shugaban matasa a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onicha a jihar Ebonyi.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun tare mutanen biyu, suka bude masu wuta sai da suka tabbatar sun mutu, sannan suka gudu

Asali: Legit.ng

People are also reading