Home Back

‘Ku daina yi wa Hukumar Alhazai Ƙagen abinda ba haka ba, a rika tantance labarai kafin a watsa – Fatima Usara

premiumtimesng.com 2024/10/5
‘Ku daina yi wa Hukumar Alhazai Ƙagen abinda ba haka ba, a rika tantance labarai kafin a watsa – Fatima Usara

Mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar NAHCON, Fatima Sanda-Usara, ta yi kiea ga mutane da su riƙa tantance rahotanni kadin su saka musamman a shafukansu na Facebook.

Usara ta yi wannan jawabi a lokacin sa take hira da rediyon Freedom.

” Ina kira ga mutane baka ɗaya da su rika tantance abubuwan da duke yaɗawa a shafukansu na yanar gizo kafin su saka ko su yaɗa shi musamman waɗanda suka shafi hukumar NAHCON da aikin Hajjin bana.

Ta kara da cewa a rika tuntuɓar hukumar da kuma ƴan jaridar da ke aiki domin watsa labarai game da aikin haji waɗanda hukumar ta amince da su.

” Ƴan jaridar na kasa mai tsarki suna ganin abinda ke faruwa kuma suna watsawa. Amma a ce kawai mutum bai san me ake ciki ba, ya zauna wuri ɗaya yana ƙagen abin da ba haka ba. Ya saɓa wa karantarwar addini.

A ƙarshe ta roki ma’aikatan hukumar na ciki da na wucin gadi su yi haƙuri da yadda abubuwa ke gudana a hukumar musamman wanda ya shafi harkar kuɗi.

Ta ce hukumar na fama da ƙarancin kuɗi saboda haka ba za ta iya biyan su kuɗi kamar yadda take yi a baya ba. Duk abinda aka samu a yi hakuri da shi.

People are also reading