Home Back

HAJJIN BANA: Hajjin 2024 ya koma Naira miliyan 8.5 bayan an yi ƙarin Naira miliyan 1.9

premiumtimesng.com 2024/4/30
Hajji
Hajji

Hukumar Alhazan Najeriya ta sake ƙara kuɗin tafiya aikin Hajjin 2024, tare da bada dalilan tashin gwauron zabin da dala ta yi.

Aƙalla maniyyata 49,000 ne suka biya Naira miliyan 4.9 kowanen su, kuɗin tafiya aikin Hajji.

Sai dai kuma a yanzu an sake yi masu ƙarin Naira miliyan 1.9 da ake so kowa ya gaggauta biya daga nan zuwa ranar Alhamis, 28 ga Maris.

A yanzu dai an yanka kuɗin zuwa aikin Hajji a matsayin Naira miliyan 8.5.

Wannan ƙarin kuɗi ya na cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran NAHCON, Fatima Sanda-Usara ta bayyana, a ranar Lahadi.

Da ta ke bayyana dalilin ƙarin har na kusan Naira miliyan biyu, Fatima ta danganta matsalar da karyewar darajar Naira da kuma tashin gwauron zabin da farashin dala ta yi a kasuwar canji.

A jiya dai an sayar da Dala 1 Naira 1,474.

Maniyyata 49,000 kowanen su ya biya Naira miliyan 4.9 lokacin da dala ta na Naira 897 a bankuna.

NAHCON ta ce ta yi bakin ƙoƙarin ganin farashin ya tsaya bai ƙaru ba, amma abin ya fi ƙarfin hukumar, domin a yanzu dala ta na N1,474.

A yanzu kenan kowane maniyyaci sai ya cika N1,918,032.91. Sannan kuma an umarce su kowa ya biya cikin kuɗin daga yau zuwa ranar Alhamis, ƙarfe 11:59 na ranar 28 ga Maris, 2024, idan ba haka ba kuwa, sai dai ya hakura, sai wata shekara kuma.

Wannan ne dai ƙari na uku da NAHCON ta yi a cikin ‘yan watanni.

People are also reading