Home Back

KAI TSAYE: Yadda Wasan Real Madrid da Barcelona Ke Gudana: 1–1

legit.ng 2024/5/18

Komai na iya faruwa a El Clasico

Real Madrid dai na da maki a teburin gasar kuma za ta iya dorawa kan nasararta a gasar La Liga, yayin da Barcelona ta samu cikas bayan shan kaye a wasanta da PSG.

Real za ta yi nasara ko da an tashi wasan da kunnen doki, amma Barca na bukatar maki uku. Yanzu da aka taken wasan, bari mu yi kallo muga abin da zai faru. Ku biyo mu sau da kafa.

Za mu bibiyi kafar yada labaran wasanni ta NBC Sport domin kawo maku wasan kai tsaye.

Real Madrid 0-1 Barcelona (Minti na 6)

Jarumin tsakiyar mako shine zakaran wasan farko. Farawa da iyawa har Barca ta zura kwallo daya a ragar Madrid.

Andriy Lunin, wanda ya yi fice sosai a Man City a tsakiyar mako, bai iya kai wa ga kwallo ba, amma Andreas Christensen ya tashi sama da Toni Kroos ya kai zura kwallon da ka.

Fenariti ga Real Madrid (Minti 18)

Vazquez ne ya ke rike da kwallo kusa da matashin tauraron Barca Pau Cubarsi ya bar kafarsa a kasa don kokarin hana wucewa.

Madadin hakan, Vazquez ya tabbatar ya yi tuntuɓe da ƙafar Cubarsi inda ya fadi, kuma an ba da bugun fanareti.

Vini ya zura kwallon. Yanzu muna 1-1.

People are also reading