Home Back

‘Yan Ta’adda Sun Kakaba Harajin N100,000 Ga Kowane Manomi A Wasu Yankunan Kaduna

leadership.ng 2024/6/28
'Yan Bindiga

‘Yan bindiga sun nemi manoman Unguwar Jibo da Nasarawa a Karamar Hukumar Kachiya ta Jihar Kaduna da su tara Naira 100,000 kowannensu a matsayin sharadin da zai sa su yi noma, wannan ya zama kamar jan kunne ne game da bayanai da suke ba wa sojoji na mafakarsu da kuma motsinsu.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa, baya ga kauyuka biyu na Unguwar Jibo da Nasarawa, manoman da ke makwabtaka da kauyuka uku da suka hada da Gidan-Makeri da Hayin Dam da Dogon-Daji da ke karkashin Karamar Hukumar Kagarko an dora musu nauyin tara Naira 100,000 kowannensu.

Majiyar ta kara da cewa, “Baya ga Naira 100,000 da aka bukaci kowane manomi ya biya, ‘yan fashin sun kuma ce manoman su rika sayo musu kayan abinci da magunguna duk bayan sati biyu a matsayin sharadi na biyu kafin a bar su su yi noma.”

Daya daga cikin shugabannin al’ummomin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da ci gaban wannan al’amari.
Ya ce, “Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata, wasu manoma a Unguwar Jibo da Nasarawa wasu ‘yan bindiga sun fatattake su daga gonakinsu bayan sun yi zargin cewa manoman ne ke da hannu wajen bai wa sojoji bayanansu.

“Matsalar ita ce kashi 95 na mutanenmu manoma ne. Yanzu da aka ce su ba da Naira 100,000 kowannensu ya jefa al’ummarmu cikin rudani.”

Don haka al’ummomin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki ta hanyar tura sojoji domin kare su.
Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Kaduna, SP Hassan Mansur, bai ce komai game da faruwar lamarin ba.

People are also reading