Home Back

An sanya wa wani yaro mai fama da farfaɗiya na'ura a kwakwalwarsa

bbc.com 2024/7/5
Oran with his mum, Justine, and siblings
Bayanan hoto, Oran na rayuwa da mahaifiyarsa, ɗan uwansa da kuma yar uwarsa
  • Marubuci, Fergus Walsh
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Medical editor

Wani yaro mai farfaɗiya ya zama na farko da aka saka wa na'ura a ƙwaƙwalwarsa domin rage raɗaɗin matsalar da yake da ita.

Na'urar, wadda ke aika sako zuwa can cikin kwakwalwarsa, na rage masa farfaɗiyar da yake da ita zuwa kashi 80.

Mahaifyarsa, Justine, ta faɗa wa BBC cewar ɗanta na cike da farin ciki "kuma rayuwarsa na cikin annashuwa".

An yi aikin saka masa na'urar ne a watan Oktoba, a matsayin wani ɓangare na gwaji a asibitin Great Ormond Street da ke Landan lokacin da yaron mai suna Oran - ke da shekara 12 - inda yanzu kuma yake da 13.

Oran wanda ya fito daga yankin Somerset, yana fama da wani nau'i na matsalar farfaɗiya wanda ya samu tun yana shekara uku.

Tun bayan wannan lokaci, ya fuskanci ɗaukewar numfashi da dama a kowace rana wanda kuma ya zarce zuwa ɗaruruwa.

Lokacin da muka fara yin magana da mahaifiyar Oran a bara, kafin a yi masa aiki, ta bayyana yadda matsalar farfaɗiya ta dabai-baye rayuwar Oran: "Matsalar ta hana shi samun sukuni ɗaukacin yarintarsa."

Ta faɗa mana cewa Oran ya fuskanci nau'i daban-daban na farfaɗiya, cik har da faɗuwa ƙasa, ta-da hayaniya, da kuma suma.

Ta ce a wasu lokutan numfashinsa na ɗaukewa, inda har sai an buƙaci taimakon gaggawa na lafiya kafin a farfaɗo da shi.

Oran yana kuma fama da galahanga, sai dai Justine ta ce farfaɗiya ita ce babbar matsala da yake fuskanta: "Ɗana ya tashi da hazaka tun yana shekara uku, sai dai watanni kaɗan bayan gamuwa da matslar farfaɗiya, ya rasa kwazonsa."

Oran na cikin wani shiri na CADET - wanda ke aikin gwajin wata nau'ra a cikin kwakwalwar masu farfaɗiya domin samun kariya.

Haɗin gwiwar ta kunshi asibitin Great Ormond Street, University College London, asibitin Kings College da kuma Jami'ar Oxford.

Wani kamfani ne mai suna Amber Therapeutics da ke Birtaniya ya kirkiri na'urar.

Yadda na'urar ke aiki

Graphic showing where the device sits in the skull
Bayanan hoto, Na'urar na ratsa sassan kwakwalwa

Ɗaukewar numfashi sakamakon farfaɗiya ko wani abu na faruwa ne lokacin da jijiyoyin kwakwalwa suka ɗan samu matsala.

Na'urar, wanda ke aika sako zuwa kwakwalwa, na da zimmar toshe ko kuma dakatar da matsalar da ke faruwa a cikin kwakwalwa.

Kafin a yi wa Oran tiyata, mahaifiyarsa ta faɗa mana cewa: "Ina so ya sake samun farin ciki da ya rasa sakamakon farfaɗiya. Ina so ɗana ya dawo kamar yadda yake a baya."

Tiyatar, wadda ta ɗauki tsawon sa'a takwas, an yi ta ne a watan Oktoban 2023.

Tawagar likitocin karkashin jagorancin wani kwararre kan ɓangaren kwakwalwar yara, Martin Tisdall, ta saka wasu na'urori biyu zuwa can cikin kwakwalwar Oran.

Surgeon showing where the neurostimulator sits in a model of a skull
Bayanan hoto, An saka na'urar cikin kasusuwa

Martin Tisdall ya faɗa wa BBC cewa: "Muna fatan binciken da muka gudanar zai ba mu damar gano ko irin wannan na'urar za ta iya yin amfani wajen magance matsalar farfaɗiya da kuma duba yiwuwar sake samar da wata na'ura, wadda za ta yi tasiri a wajen yara.

"Muna fatan hakan zai rage matsalolin da ka iya tasowa."

Waɗanda suka kunshi rage barazanar cutar bayan yin tiyata, ko kuma idan na'urar ta ki aiki.

Asalin hoton, Justine Knowlson

Oran relaxing as his neurostimulator charges wirelessly
Bayanan hoto, Za a iya yin cajin na'urar da abin jin kiɗa da ke kan Oran

An bai wa Oran wata ɗaya kafin ya samu sauki daga tiyatar da aka yi masa, kafin a kunna na'urar.

Idan aka kunnata, Oran ba zai ji kamar akwai wani abu ba. Kuma zai iya yin cajin na'urar a kowace rana ta hanyar amfani da abin jin kiɗa, lokacin da yake tare da abubuwan da ke sa shi farin ciki, kamar kallon talabijin.

Mun ziyarci Oran da iyalansa watanni bakwai bayan yi masa aiki domin ganin yadda rayuwa take kasancewa. Justine ta faɗa mana cewa an samu gagarumin nasara dangane da matsalar farfaɗiya da Oran ke fama da ita: "A yanzu yana cikin lafiya ba tare da fuskantar wata matsala ba."

Matsala da yake samu da dare ma ta takaitaccen lokaci ne kuma ba mai raɗaɗi bane".

"Yana komawa rayuwarsa ta baya sannu a hankali," in ji mahaifiyarsa.

Martin Tisdall ya ce: "Muna farin ciki cewa Oran da iyalansa sun ga gagarumin sauyi daga tiyatar da aka yi masa kuma ta inganta rayuwar ɗansu."

Yanzu, Oran na ɗaukar darussa na koyon tuki, wanda kuma yake jin ɗaɗinsa.

Duk da cewa akwai ma'aikaciyar jinya da abin taimakawa wajen yin numfashi a kusa, da kuma ɗaya daga cikin malamansa, babu wanda aka buƙace shi zuwa yanzu.

People are also reading