Home Back

SHIRIN RAYA BIRNIN KANO: Gwamna Abba ya aza harsashin ginin katafariyar gadar ƙasa da ta sama a Ƙofar Ɗan’Agundi da Tal’udu

premiumtimesng.com 2024/5/20
Ƴan Adawa su jira su ga irin abinda zan yi wa Kanawa a cikin wa’adin mulki na tukunna – Gwamna Yusuf

Gwamna Abba Kabir-Yusuf na Jihar Kano ya aza harsashen ginin katafariyar gadar sama da ta ƙasa mai hawa biyu a Ƙofar Ɗan’Agundi, wacce ta na ɗaya daga cikin ayyukan raya birni da ya bijiro da su, domin sauƙaƙa cinkoson ababen hawa a cikin birni da kewaye.

Gwamna ya kai ziyara a wurin da za yi gasar a ranar Lahadi, tare da wasu kwamishinonin sa. Ya ce zai maida Kano abin birgewa kuma birni mai kwarjini a ido.

A ranar 23 ga Disamba, 2023 ne Gwamna Abba ya bayar da kwangilar aikin ga kamfanin CCG Nigeria Limited, bisa sharaɗin za a kammala aikin cikin watanni 18.

An bayar da kwangilar aikin tare da irin ta wadda ita kuma za a gina a randabawul na Tal’udu a cikin Kano, ita ma domin sauƙaƙa cinkoson ababen hawa.

“Mun samar da hanyoyin da masu ababen hawa za su riƙa bi domin kewayewa daga bin wannan wuri. Muna kuma so a kiyaye da doka da ƙa’idoji domin wucewa lafiya, kuma a ƙyale masu aiki su yi aikin su a tsanake.”

Daga nan kuma Gwamna Abba ya aza harsashen ginin gadar Tal’udu, wadda za a gina a kan Naira biliyan 12.

Ita ma wannan gadar za ta kasance irin ta Ƙofar Ɗan’Agundi ce.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Abba, Sanusi Bature ya fitar a ranar Litinin, ya ce ayyukan raya ƙasa su na da muhimmanci ga Gwamnatin Abba Kabir-Yusuf.

Ya ce baya ga ɓangaren ilmi, wannan fanni ne na raya ƙasa ya fi bai wa muhimmanci.

Manajan Kamfanin CGC Nigeria Limited, Mista Gee Wang da Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, Marwan Ahmad, sun bayyana wa manema labarai ce lallai a cikin watanni 18 ɗin da aka yi yarjejeniya za a kammala aikin.

People are also reading