Home Back

An Aike Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi

leadership.ng 3 days ago
An Aike Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi

Ƴansanda a jihar Bauchi sun kama wani mutum mai suna, Bala Mohammed, ɗan shekara 67 kan zargin yi wa wasu ‘yan mata biyu fyaɗe a jihar Bauchi bayan ya yi musu roman baka kan zai ba kowacce daga cikinsu da kuɗi N500.

LEADERSHIP HAUSA ta samu labarin cewa, Bala yana amfani da dabarunsa ya yi wa ‘yan mata fyade, wanda wannan shi ne kusan karo na biyar kafin wannan.

Kakakin Rundunar ƴansandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya ce, iyayen yaran da abin ya shafa sun shigar da kara kan Bala Mohammed kan zargin yi wa yaran su fyaɗe.

“A ranar 22 ga watan Yunin 2024 da misalin, wani mai suna, Abubakar Danladi ɗan shekara 43 da Umar Ismail mai shekaru 65 daga Unguwar Mahaukata ta jihar Bauchi, sun kai rahoto hedikwatar ‘yansanda ta ‘A’, cewa Bala Mohammed mai shekaru 67 sun kama shi yana lalata da ‘ya’yansu mata da wata da aka laƙana wa suna Safiya (ba sunan gaskiya ba) mai shekaru 17 da Hassana (ba sunan gaskiya ba ne) me shekaru 16 duk masu adireshi ɗaya, kan ya shigar da su dakinsa yana lalata da su kan Naira dari biyar (N500) tsawon kwanaki biyar.

“Lokacin da ake yi wa wanda ake zargi tambayoyi, ya amsa aikata laifin,” cewr sanarwar.

Wakil ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike, inda daga nan ne za a bayyana wanda ake zargin sannan a gurfanar da shi a gaban kotu domin gurfanar da shi gaban kuliya.

A wani labarin makamancin wannan, Kakakin ‘Yansandan Bauchi, Wakili ya ce wani suna Suleiman Musa, mai shekaru 28, ya lalata wata yarinya ‘yar shekara 9 ta hanyar fyade a cikin dakinsa ta hanyar tursasa ta da ƙarfin tsiya.

Lokacin da yake amsa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikata wa, har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike, inda za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu don gurfanar da shi a gaban shari’a.

People are also reading