Home Back

Yadda Dangote Ya Raba Tallafin Abinci Na Naira Biliyan 15, Jihar Kano Ta Samu Kaso Mafi Tsoka

leadership.ng 2024/5/17
Yadda Dangote Ya Raba Tallafin Abinci Na Naira Biliyan 15, Jihar Kano Ta Samu Kaso Mafi Tsoka

A wani mataki na rage radadin talauci a tsakanin al’umma, a kwanan nan Gidauniyyar Dangote ta kaddamar da tallafin rabon abinci a jihohin kasar nan inda mutane akalla miliyan daya suka amfana.

Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da cewa tallafin zai game dukkanin kananan hukumomin kasar nan 774, na kimanin buhunan shinkafa milyan daya mai nauyin kilo 10.

Jihar Kano ta samu kaso mafi tsoka inda mutane 120,000 suka amfana.

Haka zalika rabon shinkafa mai kilo 10 zai ci gaba a dukkanin sauran kananan hukumomi na Jihar Kano.

Bikin kaddamar da rabon abincin dai ya gudana ne a dakin taro na fadar Gwamnatin Kano da shugaban rukunonin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya samu halarta da kuma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

A cewar Alhaji Aliko Dangote , sun ga dacewar raba kayan abincin ne ba wai kawai don magance matsalar yunwa ba, har da batun saukaka wa al’umma wajen gudanar da rayuwa a kasa baki daya.

“Hakan kuwa ya zama wajibi duba da muhimmancin zumunci da ‘yan’uwantaka da ke tsakanin mu, da kuma hadin kai a wannan lokaci da ake fusakantar kalubalen rayuwa.

“A wannan wata na Ramadan, lokaci ne da muke sadar da halayen nagarta, wanda ke taimakawa wajen tallafawa al’umma”.

“Ina da kwarin gwuiwar sanar da ku cewa wannan tallafin na yanzu na musamman ne, duk da cewar mun yi irin sa a kasa da wata guda da ya gabata, amma muka ga dacewar sake tallafa wa al’umma musamman a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan.

Attajirin Alhaji Aliko Dangote, ya shaida wa gangamin taron al’ummar cewa wannan kari ne a kan tallafin da ya gudana na mutane dubu goma da ake ciyarwa kullum a Jihar Kano, yace Tallafin shinkafar mai kilo goma da ya kaddamar kimanin miliyan Ɗaya, ya lakume kudade Naira bilyan 15 a kasa baki daya.

Da yake jawabi Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shirin rabon tallafin kayan abincin inda yace yazo a dai-dai lokacin da dimbin al’umma ke bukatar hakan.

Gwamnan ya bukaci kwamitin da aka dora wa nauyin rabon kayan abincin ciki har da hukumar HISBAH ta jiha da ya maida hankali wajen aiwatar da aikin cikin gaskiya da rikon amana don cimma manufar shirin.

“Wannan shirin zai taimaka wajen rage saukaka rayuwa”, a cewar Gwamnan Kano. Inda ya sake kara jinjina kaso mafi tsoka da jihar ta samu.

Zouera Yousoufou da ke zaman shugaban gidauniyyar ta Aliko Dangote ta yi karin haske kan kokarin Alhaji Aliko Dangote wajen tallafa wa al’umma, inda ya ce shakka babu gidauniyyar za ta ci gaba da bai wa wannan bangaren muhimmanci.

“Mu ne a gidauniyyar Dangote muke ganin ya zama wajibi a sanar da al’umma irin kokarin da yake yi don sauran al’umma masu kudi su kwaikwayi halayensa nagari na tallafa wa al’umma”, a cewar Yousoufou.

Rabon tallafin kayan abincin da Alhaji Aliko Dangote ya jagoranta na shinkafa miliyan Daya da ke dauke da kilo goma na nuni da kokarinshi wajen rage radadin rayuwa da marasa galihu ke fuskanta da kuma kara dankon zumunci a tsakanin al’umma.

People are also reading