Home Back

Fahimtar Manufar Kasar Sin Ta Yin Kwaskwarima A Sabon Zamani ——Za A Cimma Buri Idan Aka Kyautata Aiki Bisa Yanayi, Za A Samu Ci Gaba Idan Aka Kiyaye Yin Kirkire-kirkire

leadership.ng 2024/8/24
Fahimtar Manufar Kasar Sin Ta Yin Kwaskwarima A Sabon Zamani ——Za A Cimma Buri Idan Aka Kyautata Aiki Bisa Yanayi, Za A Samu Ci Gaba Idan Aka Kiyaye Yin Kirkire-kirkire

A watan Disamban shekarar 2012, Xi Jinping wanda ya hau karagar mukamin babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, a taron wakilan jam’iyyar karo na 18, ya bayyana a birnin Shenzhen, birnin dake kokarin yin kwaskwarima, da bude kofa ga kasashen waje cewa, “yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, muhimmin aiki ne da aka sa gaba, wanda ke da babbar alaka da makomar Sin”. 

Bayan hakan, kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta Sin, bisa jigon shugaba Xi Jinping, ya gabatar da shirin yin kwaskwarima mai zurfi a dukkan fannoni, wanda hakan ya alamta bude sabon lokacin yin kwaskwarima a dukkan fannoni bisa tsari.

Bayan shekaru 10, wato a shekarar 2022, a gun taron wakilan JKS karo na 20, an gabatar da manufar zamanintar da kasar Sin, da abubuwan dake shafar manufar. Inda Xi Jinping ya bayyana cewa, “Zamanintarwa irin ta Sin ta dace da yanayin kasar Sin. Ya kamata mu kara yin imani da yin kirkire-kirkire, don bude sabon babi na raya kasa ta zamani a dukkan fannoni dake bin tsarin gurguzu.”

A watan Mayun bana, shugaba Xi ya sake tsai da kudurin cewa, yin kwaskwarima, da bude kofa ga kasashen waje, muhimmin mataki ne na tabbatar da zamanintarwa irin ta kasar Sin. Wannan ya shaida cewa, yin kwaskwarima mai zurfi a dukkan fannoni, ya shiga sabon lokaci mai muhimmanci, inda aka mai da hankali ga wani abu mai muhimmanci, wato kiyaye dabi’a da yin kirkire-kirkire.

Shugaba Xi ya taba bayyana cewa, “Ko da yake ana samun babban canji a lokaci, ya kamata mu kiyaye dabi’armu, da yin kirkire-kirkire, da kuma yin kokarin samun ci gaba. Wanda ya yi kirkire-kirkire, zai samu nasara.”

Yayin da ake aiwatar da manufar, shugaba Xi ya mai da hankali ga aikin raya tsari, da yin kokarin kafa tsarin aiwatar da manufofi bisa kimiyya yadda ya kamata, ta yadda za a inganta tsarin tafiyar da harkokin kasa na zamani. (Zainab Zhang)

People are also reading