Home Back

An yi cinikin ƴan ƙwallo £185.5m a Premier a bana fiye da watan Janairu

bbc.com 4 days ago
EPL transfer

Asalin hoton, Getty Images

Tuni ƙungiyoyin Premier League suka kashe ƙudi da yawa a kwana hudu a bana - an yi cinikin £185.5m fiye da abinda aka kashe a watan Janairu.

Ƙungiyoyi da yawa sun yi ciniki tun kafin ranar Lahadi, inda ranar Litinin aka sanar da wadanda aka ɗauka da wadanda aka sayar.

To amma ƙungiyoyin sun yi kokarin kaucewa ɗebe musu maki, idan ba su kashe ƙudi daidai samu ba - wa'adin da ya cika ranar 30 ga watan Yuni.

Sai a ranar Juma'a 30 ga watan Agustan 2024 za a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo, tuni kuma ƙungiyoyin suka tsara yin cefanen ƴan wasa da wuri.

Ƙungiyoyin da suka fi yin cefane tun daga ranar 14 ga watan Yuni da aka buɗe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo, sun hada da Aston Villa da Everton da Chelsea da kuma Newcastle United.

Villa ta sanar da faɗuwa kasuwanci £119m tun daga 31 ga watan Mayun, 2023, hakan ya sa ta cefanar da wasu ƴan wasa don kar ta karya ka'ida.

An kwashe maki shida a Everton a kakar da ta wuce, bayan karya doka da ta yi har karo biyu, yayin da Chelsea ta kashe fam biliyan daya tun bayan da Todd Boehly ya mallaki ƙungiyar a 2023.

Yawancin cinikin Chelsea kan kwantiragin kaka shida ta dunga yi, wadda ta dunga raba yadda za take biya kudin - hakan ya sa ba ta karya dokar kashe kudi daidai samu ba.

Wasu rahotannin sun ce Newcastle ta haura da £50m na ka'ida a ranar Asabar da safe - hakan ya sa ta ɗauki mataki kafin a sameta da laifin da za a kwashe mata maki.

People are also reading