Home Back

Takaitaccen Nazari A Kan Yadda Ake Noman Karas A Nijeriya

leadership.ng 2024/5/1
Takaitaccen Nazari A Kan Yadda Ake Noman Karas A Nijeriya

Ko shakka babu, ana yin noman Karas yadda ya kamata a Nijeriya, sannan ya kasance kayan lambu na biyu a duniya da aka sani baya ga Dankali, kazalika kuma yana daukar daga kimanin kwana 70 zuwa 80 kafin ya fara nuna.

Haka zalika, Jihar Filato ce a kan gaba wajen nomansa a duk fadin wannan kasa, sakamakon yanayi da jihar ke da shi mai matukar kyau wanda ya da ce da nomansa.

Yadda Ake Nomawa

Ana samun nau’ikan Irinsa da dama a Nijeriya, wadanda suke samar da amfanin gona mai tarin yawa, wasu daga cikin nau’ikan Irin da ake kira a turance sun hada da ‘Danbers, Chantanay, Nantes, Armsterdam’ da sauran makamantansu, wadanda kuma sun kasance suna bukatar ingattaciyar kasar noma.

Ganin cewa, Irinsa na da wuyar sha’ani yana kuma son kulawar da ta dace, ya zama wajibi a gyara gonar don shuka Irin yadda ya dace, haka nan; ya fi dacewa a shuka Irin a kan Kunyoyi yadda jijiyoyinsa za su samu sukunin shiga cikin kasar da aka shuka shi.

Amfanin Karas:

Yana da matukar amfani sosai ga rayuwar Dan Adam, domin kuwa ana yin amfani da shi wajen hada miya ko abinci tare da sarrafa shi zuwa kayan zaki, haka nan yana dauke da wasu sinadaran hada magunguna  da suka hada da ‘thiamine da riboflabin’.

Har ila ya, cin sa tsura na taimakawa wajen kara lafiyar jikin  dan Adam tare da da dai-daita sinadarin ‘cholesterol’ da ke rage kiba a jikin mutum.

Bugu da kari, yana dauke da sinadarin ‘beta carotene, bitamins A, D, C, E, K, potassium da kuma minerals’, wadanda suke taimaka wa wajen karin gani na Ido tare da kara gyara fatar jiki.

Har ila yau, Karas na dauke da sauran sinadaran da ke kara wa Dan Adam karfin jiki da wadanda suka hada da: ‘fat, protein, carbohydrates, sodium, zinc, phosphorus, potassium, manganese, calcium and iron’.

Yawan ruwan da ke jikinsa, ya kan kai  kashi 88 a cikin 100, wanda yake dauke da sindarin ‘protein da ya kai kimanin kashi 0.9 a cikin dari, sai kuma sinadarin ‘fibre’ da ya kai kashi 2.8 a cikin dari, inda sinadarin ‘fat’ ke dauke da kashi 0.2 a cikin dari, sai kuma sinadarin ‘carbohydrates’ da kashi 9 cikin dari.

Canjin Yanayi:

Karas ya fi son yanayi mai sanyi, musamman wanda ya kai  ma’unin yanayi daga 16 zuwa 20, amma ma’aunin yanayin da ya wuce 28, na rage masa saurin girma kuma idan aka shuka Irin yana kaiwa daga kimanin kwana bakwai zuwa 21 kafin ya fara fitowa daga cikin kasa.

Yadda Ake Shuka Shi:

Bayan an tona kasa an zuba Irin a yayin shuka shi, ana rufe shi ne a hankali, kazalika wasu manoman kan yi wa gonar da za su shuka shi ban ruwa har zuwa tsawon awa ashirin da hudu kafin su shuka Irin, musamman don ya samu danshi sosai. Sannan, ana kuma bukatar manomi ya nemi shawarar masana a kan wannan Iri da kuma Takin da ya dace ya yi amfani da shi.

Har ila yau, za a iya zuba Takin Gargajiya; bayan wata guda da shuka shi, domin amfanin ya yi saurin girma.

Ban Ruwa:

Karas na bukatar yawan ruwa, musamman a lokacin noman rani, don ya girma da wuri; kana kuma ana so bayan an shuka shi a tabbatar da an yi masa ban ruwa, domin ya kasance yana dauke da danshi.

Lokacin Da Ya Fi Dacewa Da Girbin Karas:

Ana girbe shi ne, bayan an tabbatar da cewa ya gama girma yadda ya kamata, sannan manomi zai iya barin sa a gona ba tare da ya girbe shi ba, sai dai kuma ana bayar da shawara cewa; ka da a bar shi ya jima a inda aka shuka shi  ba tare da an girbe shi ba, don gudun ka da ya yi tauri. Haka nan, ana  girbe shi ne bayan jijiyarsa ta kai girman kimanin mita 1.8 ko kuma fiye da haka.

Ribar Nawa Manomi Yake Samu?

Bisa binceken da aka yi a kwanakin baya na tsadar farashin noman Karas, an kiyasta cewa kowace kadada daya; ta kai kimanin dala 10,600.

Nawa Ake Kashewa Wajen Noman Karas A Kadada Daya?

Kudaden da ake kashewa ciki har da na hayar gona a kowace Kadada daya, sun kai kimanin dala 4,200 zuwa dala 5,000, inda kuma sarrafa shi a kadada daya ya doshi daga dala 1,500 zuwa dala 2,000

People are also reading