Home Back

Yadda Za A Yaki Ciwon Sikila A Nijeriya Daga Tushe – Hajiya Badiyya

leadership.ng 2024/7/24
sikila

Shugabar cibiyar tallafa wa masu lalurar amosanin jini wanda akafi da sikila da ke Jihar Kaduna, (SCPHPC), Hajiya Badiyya Magaji Inuwa, ta bayyana matakan da ya kamata a bi domin a yaka ciwon sikila daga tushe a kasar nan.

Ta ce, za iya cimma wannan nasarar ce idan ministan ilimi ya bayar da umarni a saka darasin koyar da daliban makarantar sakandare a cikin manhajar koyar da daliban domin a yaki cutar ta sikila daga tushe.
Badiya wadda ake yi wa lakabi da Maman Sikila, ta bayyana hakan ne a hirarta da LEADERSHIP Hausa a Kaduna.

Ta yi nuni da cewa, inda za a samu a saka darasin a cikin manhajar karatu da za a koyar da daliban, musamman daga matakin dalibai ‘yan aji uku na sakandare, wadanda a wannan lokacin ne suka fara girma, suka kuma fara sanin mece ce soyayya kafin su shiga aji biyar, hakan zai taimaka wajen dakile ciwon.

Kazalika, Badiyya ta ce ta hakan ne za a ilimatar da daliban domin su san hadarin ciwon da yadda za su kauce wa cutar.

Ta ci gaba da cewa ta wannan hayar za a taimaka matuka wajen kara yakar ciwon, musamman duba da irin tsangwamar da ake yi wa masu fama da ciwon a cikin al’umma.

ta ce za ta rubuta wasiki zuwa ga shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar dokokin Jihar Kaduna don gabatar da kudIri a zauren majalisar kan bukatar a kirkiro da dokar da za ta sa a rinka daukar jinin yara kafin a sa su a makarantar firamare a kuma hada da takardun haihuwarsu, inda hakan zai nuna irin nau’in jininsu.

Badiyya ta nanata muhimmancin yin gawaji kafin a yi aure, wanda ta ce hakan zai kare haifar yara masu masu cutar.

People are also reading