Home Back

SHARI’AR SARAUTAR KANO: Lauyan Aminu Ado ya janye daga wakiltar sa a Babbar Kotun Kano

premiumtimesng.com 2024/10/5
Gina Jami’oi masu zaman kansu zai sa dalibai samun guraben Karatu – Sarkin Kano, Aminu Bayero

A ci gaba da shari’ar dambarwar ikon masarautar Kano, Abdul Muhammad wanda shi ne lauyan tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Aminu Ado, ya bayyana janye kan sa daga ci gaba da kare tsohon sarkin a shari’ar da ke gudana a Babbar Kotun Kano.

A ranar 27 ga Mayu ce dai Antoni Janar na Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Kano, Ɗaukacin Majalisar Dokokin Kano suka shigar da ƙara ta hannun lauyan su Ibrahim Isah-Wangida, a Babbar Kotun Kano.

A ranar ce dai suka nemi kotun ta umarci Aminu Ado da sauran sarakunan da ta tuɓe tare da shi, na Gaya, Ƙaraye, Rano da Bichi cewa su daina kiran kan su sarakuna.

Cikin waɗanda aka maka kotun har da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Daraktan SSS, NSCDC da kuma Rundunar Sojojin Najeriya.

Yayin da aka kira shari’ar domin saurare, sai lauyan Aminu Ado, Muhammad Wandiga ya shaida wa kotu cewa to ai shi ya shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara a ranar 3 ga Yuni, inda ya nemi kotu ta dakatar da ƙarar da aka maka Aminu a Babbar Kotun Kano.

Daga nan sai ya nemi Babbar Kotun Kano ɗin ta dakatar da shari’ar har sai ta ji hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke tukunna.

Sai dai kuma lauyan waɗanda aka shigar da ƙara na 3, na 4 da na 5, Hassan Tanko-Ƙyaure, ya nemi a ƙara lokaci zuwa 2 ga watan Yuli.

Ya roƙi kotu ta jingine Dokar Majalisar Dokokin Kano wadda aka yi wa gyara a 2024, ya na mai cewa ba a bi ƙa’ida wajen zartas da dokar ba.

Lauyan Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Sunday Ekwe, ya shaida wa kotu cewa ba su da wata jayayya, sun bar wa kotu ta yi hukuncin ta.

Da take yanke hukunci tun farko, Mai Shari’a Amina Aliyu ta ƙi amincewa da jingine shari’ar kamar yadda lauyan Aminu ya nema.

Mai Shari’a ta ɗage shari’a zuwsa ranar 18 ga Yuli domin amsa buƙatar ƙarin lokacin da aka nema.

People are also reading