Home Back

Rikicin Masarauta: An Ba Gwamna Abba Shawara Kan Abin da Ya Kamata Ya Yi

legit.ng 2024/7/2
  • Wata ƙungiya ta fito ta ba gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf shawara yayin da ake cikin rigimar masarautar Kano
  • Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan da ya mayar da hankali wajen sauke nauyin da ke wuyansa na al'ummar jihar Kano ba ya tsaya yana cece-kucen siyasa
  • Ta nuna kuskuren da gwamnan ya yi na sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata ƙungiya mai suna Arewa Leadership Foundation, ta shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya mayar da hankali kan mulkin jihar Kano.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan da ya mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka addabi mutanen jihar Kano.

Kungiya ta ba Gwamna Abba shawara
Kungiya ta ba Gwamna Abba na Kano shawara Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Ƙungiya ta gargaɗi Gwamna Abba

Ƙungiyar ta shawarci gwamnan da ya daina mayar da hankali kan abubuwan da ba za su kawo ci gaba a jihar ba, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Dakta Isa Abubakar, ƙungiyar ta gargaɗi gwamnan da ya daina kallon Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin matsala a wajensa.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa a matsayinsa na gwamna babban nauyin da ya rataya a wuyansa shi ne yi wa al’ummar jihar Kano aiki, ba wai cece-kucen siyasa ba.

"Mun damu kan yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke neman ɗaukar fansa wanda hakan ya sanya yake ta gallazawa Ganduje da sauransu."
"Hakan ya sanya hankalin gwamnan ya rabu inda ya kasa cika alƙawuran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓensa."
"Rikicin masarautar Kano wanda gwamnan ya sake naɗa Sanusi II ya ƙara sanyawa al'amura sun taɓarɓare."
"Hakan ba wai kawai kawo rarrabuwar kai da rikici ya yi a jihar ba, har da kawar da hankalin gwamnan daga aiwatar da muhimman ayyukan da suka dace."

- Dakta Isa Abubakar

Wace shawara aka ba Gwamna Abba?

Ƙungiyar ta shawarci Gwamna Abba da ya mayar da hankali wajen sauke nauyin da ke wuyansa na al'ummar Kano ba neman ɗaukar fansa ba.

Ƙungiyar ta kuma gargaɗi Gwamna Abba da ya dawo da hankalinsa wajen kawo abubuwan more romon dimokuraɗiyya da suka haɗa da inganta harkar kiwon lafiya, ilmi ga al'ummar jihar Kano.

NNPP ta yabi Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NNPP reshen jihar Legas ta yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarinsa na kiyaye martabar al’adun gargajiyar jihar.

Jam'iyyar ta kuma yabawa gwamnan kan sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 bayan ya tsige Aminu Ado Bayero daga sarauta.

Asali: Legit.ng

People are also reading