Home Back

‘Yan Jarida Sun Dakatar Da Kawo Rahotanni Daga Fadar Gwamnatin Kano

leadership.ng 2024/7/6
‘Yan Jarida Sun Dakatar Da Kawo Rahotanni Daga Fadar Gwamnatin Kano

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da kauracewa kawo rahoto ko wasu labarai na ayyukan gwamnatin jihar Kano.

Wannan na zuwa ne bayan zargin cin zarafi da rashin girmama aikin ‘yan jarida da gwamnatin jihar da jami’anta ke yi wa ‘yan jarida.

Ƙungiyar ta kuma soki gwamnati da mayar da kwararrun ‘yan jarida gefe tare da fifita waɗanda ba su da ƙwarewa ko kuma ƙwazo a wajen aiki.

Sakamakon haka, ƙungiyar ta ke sanar da dakatar da kawo duk wani rahoto ko labarai kan abubuwan da suka faru na gwamnati ko halartar taron manema labarai, ko yin hira da jami’an gwamnatin jihar har sai an sami cikakkiyar fahimta da kuma tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da kare lafiyarsu kafin mu ci gaba da aiki kamar yadda yake a ƙunshe cikin sanarwar.

Shugaban kungiyar, Aminu Ahmed Garko, ya jaddada muhimmancin ‘yan jarida na tabbatar da dimokuradiyya tare da yin kira ga daukacin ‘yan uwa abokanan aiki da su goyi bayan wannan shirin da kuma tabbatar da ‘yancin ‘yan Jarida.

People are also reading