Matasan N-power Za Su Sha Jar Miya, Tinubu Zai Biya Su Basukan Watanni 8
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan basukan masu cin gajiyar N-power a Najeriya.
Gwamnatin ta ce za ta iya biyan basukan da matasan ke binta na watanni takwas a karshen wannan wata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da makarantar jin kai da walwala ta fitar a shafin X.
"Masu cin gajiyar N-power za su iya samun alawus da suke bin gwamnati na watanni takwas a karshen wannan wata, ku kara hakuri."
- Ma'aikatar jin kai
Wannan na zuwa ne yayin da masu cin gajiyar N-power ke kokawa kan tulin basukan da suke bin gwamnatin a baya.
Akalla matasan na bin gwamnatin bashin watanni takwas wanda ba a biya su ba yayin da suke cikin shirin.
Daga bisani an dakatar da shirin kan binciken badakala a ma'aikatar da ake zargin Ministar jin kai, Dakta Betta Edu da mukarrabanta.
Daga bisani an dakatar Edu saboda kaddamar da bincike game da almundahana a ma'aikatar na biliyoyi.
Karin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng