Home Back

Matasan N-power Za Su Sha Jar Miya, Tinubu Zai Biya Su Basukan Watanni 8

legit.ng 2024/7/6
  • Da alamu matasa za su kwashe bayan Bola Tinubu ya juyo ta kansu kan basukan N-power da suke bin gwamnati
  • Matasa masu cin gajiyar N-power suna bin gwamnatin akalla basukan watanni takwas ba tare da biyansu ba
  • Ma'aikatar jin kai ta ce za su iya samun basukan da suke bi na watanni takwas a karshen wannan wata da muke ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan basukan masu cin gajiyar N-power a Najeriya.

Gwamnatin ta ce za ta iya biyan basukan da matasan ke binta na watanni takwas a karshen wannan wata.

Watakila masu cin gajiyar N-power za su iya samun basukansu a karshen wata
Matasan N-power suna bin gwamnati bashin watanni 8. Hoto: N-power. Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da makarantar jin kai da walwala ta fitar a shafin X.

"Masu cin gajiyar N-power za su iya samun alawus da suke bin gwamnati na watanni takwas a karshen wannan wata, ku kara hakuri."

- Ma'aikatar jin kai

Wannan na zuwa ne yayin da masu cin gajiyar N-power ke kokawa kan tulin basukan da suke bin gwamnatin a baya.

Akalla matasan na bin gwamnatin bashin watanni takwas wanda ba a biya su ba yayin da suke cikin shirin.

Daga bisani an dakatar da shirin kan binciken badakala a ma'aikatar da ake zargin Ministar jin kai, Dakta Betta Edu da mukarrabanta.

Daga bisani an dakatar Edu saboda kaddamar da bincike game da almundahana a ma'aikatar na biliyoyi.

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

People are also reading