Home Back

Gwamnatin Jigawa Za Ta Ba Manoma Tallafin N3.5bn, Ta Fadi Wadanda Za Su Amfana

legit.ng 2024/10/5
  • Gwamnatin jihar Jigawa za ta ba manoma mutum 30,000 tallafi domin bunƙasa harkokin noma domin samar da abinci a jihar
  • Majalisar zartaswar jihar ta amince da fitar da Naira biliyan 3.5 domin rabawa ga manoman a matsayin tallafin bunƙasa aikin noma
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar wanda ya sanar da hakan, ya ce tuni aka zaɓo manoman da za su amfana da tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Majalisar zartaswar jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira biliyan 3.5 a matsayin tallafi ga manoma.

Manoma mutum 30,000 ne za a ba tallafin domin bunƙasa aikin noma a jihar.

Gwamnatin Jigawa za ta ba manoma tallafi
Gwamnatin Jigawa za ta ba manoma tallafin N3.5bn Hoto: @uanamadi Asali: Twitter

Kwamishinan yaɗa labarai, matasa, wasanni da al'adu na jihar, Honorabul Sagir Musa, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron majalisar a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane tallafi za a ba manoma a Jigawa?

Ya ce tallafin wanda ya haɗa da tsabar kuɗi da kayan aikin gona, za a raba su ga zaɓaɓɓun manoman Fadama na karkara domin bunƙasa ƙarfinsu na yin noma.

A cewarsa shirin na samun tallafi daga bankin duniya a ƙarƙashin shirin farfado da tattalin arziƙi na Korona, wanda aka ƙirƙiro domin rage tasirin annobar cutar Korona.

Sagir Musa ya ƙara da cewa ma’aikatar noma da albarkatun ƙasa ta zaɓo waɗanda za su ci gajiyar su 30,000 a tsanake a ƙarƙashin shirin FADAMA IV da V domin bunƙasa samar da abinci da inganta rayuwar al’ummar karkara.

"Ana sa ran shirin ba wai kawai zai rage tasirin cutar ta korona ba, har ma zai taimaka wajen ɗorewar noma da ci gaban tattalin arziki a jiha."

- Sagir Musa

Kwamishinan ya nanata ƙudirin Gwamna Umar Namadi na samar da sana'o'i ga al’ummar Jigawa domin samun ci gaba.

Gwamnatin Jigawa za ta siya jami'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta fara shirye-shiryen sayen jami'ar Kahadijah da ke Majia domin inganta harkokin ilimi a jihar.

Hakan ya biyo bayan amincewar Gwamna Umar Namadi da rahoton kwamitin majalisar zartaswa na tayin sayen jami'ar domin ta dawo hannun gwamnati.

Asali: Legit.ng

People are also reading