Home Back

Gwamnatin Nijeriya Ta Yaba Da Ƙwazon Tawagar ‘Yan Nijeriya A Wasannin Afirka

leadership.ng 2024/5/12
AFCON 2023: Za A Kece Raini Tsakanin Nijeriya Da Cote de’Voire A Wasan Karshe Ranar Lahadi

Gwamnatin tarayya ta yaba da irin bajintar da kungiyar Nijeriya ta yi a gasar cin kofin Afrika karo na 13 da aka kammala a Ghana.

LEADERSHIP HAUSA ta rawaito cewa kungiyar ta Nijeriya ta zo ta biyu a kan teburin gasar bayan kasar Masar ke da zinare 47 da azurfa 33 da kuma tagulla 40.

Ministan wasanni, Sanata. John Owan Enoh, wanda ya mika sakon taya murna ga shugaba Bola Tinubu ga ’yan wasan a ranar Lahadi a Abuja, ya bayyana rawar da suka taka a matsayin abin yabawa.

“A madadin mai girma Asiwaju Bola Tinubu, ina yi muku barka da dawowa kasarmu mai albarka.

“Ina taya ku murna saboda irin bajintar da kuka nuna a gasar wasannin Afrika karo na 13 da aka kammala a Ghana.

Enoh ya ce “Da yawan ‘yan Nijeriya suna taya ku murna da farin ciki da irin nasarorin da kuka samu wajen sanya kasar nan a matsayin babbar cibiyar wasanni a nahiyar Afirka,” in ji Enoh.

Kasashe 52 ne suka fafata da juna domin neman lambar yabo a wasanni 29, inda Nijeriya ta zo a ta 25.

Ministan, ya jaddada bukatarsa ta gaggauta fara shirye-shiryen tunkarar gasar wasannin Afrika karo na 14 da za a yi a Masar a shekarar 2027 don ganin an yi nasara.

“A matsayinka na Ministan Ci gaban Wasanni, wanda ake yi wa lakabi da Nigeria’s GamesMaster General, na tabbata zai kasance tare da ku har abada,” in ji shi.

Ministan ya bayar da tabbacin cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da ba da fifiko kan jin dadin wasannin Nijeriya maza da mata kamar yadda aka tsara a duniya.

People are also reading