Home Back

Dangote, Elumelu Sun Samu Shiga Yayin da Tinubu Ya Rantsar da Kwamitin Tattalin Arziki

legit.ng 3 days ago
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da majalisa ta musamman da za ta kawo gyare-gyaren manufofin tattalin arziki
  • Wannan majalisar dai ta kunshi jami'an gwamnati, 'yan kasuwa da kuma mashawarta da suka hada da attajirin Afrika, Aliko Dangote
  • Ana sa ran majalisar za ta rika ganawa da Shugaba Tinubu a kowanne wata kuma za ta taimaka wajen bunkasa hako danyen mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da majalisar daidaita tattalin arziki (PECC) da aka dorawa alhakin tsara dabarun fita daga halin matsin tattalin arziki a Najeriya.

Majalisar ta hada da jami’an gwamnati, 'yan kasuwa da kuma mashawarta da suka hada da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Mista Aliko Dangote.

Tinubu ya rantsar da majalisar tattalin arziki
Tinubu ya rantsar da su Dangote a cikin majalisar tattalin arziki. Hoto: @NGRPresident Asali: Twitter

Tinubu ya rantsar da kwamitin PECC

Sauran wadanda ke cikin majalisar sun hada da shugaban bankin UBA, Tony Elumelu da shugaban kamfanin hada-hadar kudi na FDCL, Bismarck Rewane, in ji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake yi wa manema labarai karin haske bayan rantsar da majalisar, ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya ce majalisar za ta rika ganawa da shugaban kasa duk wata.

A cewar Edun, Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar PECC da ta samar da tsare-tsare da dabarun gyara tattalin arzikin kasar wadanda za a yi amfani da su a watanni shida na gaba.

Gwamnati ta ci buri kan hako danyen mai

Bugu da kari, majalisar za ta zage damtse wajen ganin gwamnati ta cika burinta na iya hako danyen mai har ganga miliyan biyu a kowace rana.

Jaridar Vanguard ta ruwaito ministan tattalin arzikin ya kuma ce akwai shirin da aka yi na batar da Naira tiriliyan 2 wajen daidaita tattalin arzikin kasar wanda ya hada da:

  1. Kashe Naira biliyan 350 domin bunkasa fannin lafiya da jin dadin al'umma
  2. Kashe Naira biliyan 500 domin bunkasa fannin noma da samar da abinci.
  3. Kashe Naira biliyan 500 domin bunkasa fannin makamashi da wutar lantarki
  4. Kashe Naira biliyan 650 domin tallafawa fannin kasuwanci na bai daya

Asali: Legit.ng

People are also reading