Murna Ta Koma Ciki, An Hallaka Amarya Mako Ɗaya Tak Bayan Ɗaura Aurenta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Amarya da ba ta wuce mako ɗaya da shiga daga ciki ba na cikin waɗanda ƴan bindiga suka kashe a harin Nnobi da ke jihar Anambra.
Rahotanni daga bakin iyalanta sun nuna cewa amaryar tana jiran dawowar mijinta daga ƙasar waje sannan ta tare, bisa tsautsayi harsashi ya same ta a harin.
Wata majiya daga iyalan marigayyar ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Punch ranar Talata amma ba a bayyana sunan amaryar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun farko dai wasu ƴan bindiga sun kai farmaki garuruwan Nnewi da ke ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa da Nnobi a ƙaramar hukumar Idemili, jihar Anambra ranar Litinin.
Maharan sun kashe mutanen da har yanzun ba a tantance adadinsu ba ciki har da ƴan banga, sun kuma jikkata wasu da dama.
Lamarin ya haifar da firgici a garuruwan biyu yayin da ‘yan kasuwa da mazauna garin suka ruga a cikin gida domin tsira daga sharrin maharan.
Sai dai duk da haka ƴan bindigar waɗanda ake kyautata zaton masu kaƙaba dokar zaman gida ne, sun buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.
Majiyar ta ce:
“Daga cikin wadanda aka kashe jiya (Litinin) a Nnobi akwai ƴar uwata, sati ɗaya kenan da ɗaura aurenta. Tana jiran mijinta ya dawo daga kasar waje ne kafin ta tare.
"Matashiya ce ƴar shekara 22 a duniya kuma ita ce ɗiya ɗaya tilo a wurin iyayenta. Lamarin akwai ban tausayi kuma ba karamar illa ya yi mana ba."
An tattaro cewa tuni dakarun ƴan sanda da ƴan banga suka bazama domin farautar maharan da nufin kamo su doka ta yi aiki a kansu.
A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun kashe mutane yayin da suke tsaka da taro a kauyen Ewehko, ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige akalla mutum biyar har lahira ido na ganin ido ranar Litinin.
Asali: Legit.ng