Home Back

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Jihohi, Sun Kama Manyan 'Yan Ta’adda

legit.ng 3 days ago
  • Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan taron manyan yan ta'adda a jihohin Imo da Kwara domin dakile ayyukan barna
  • Farmakin ya ba sojojin Najeriya nasarar cafke wasu manyan yan ta'addan da suka fitini al'umma da ayyukan ta'addanci
  • Har ila yau, rundunar sojin ta bayyana irin makaman da ta kwace wajen yan ta'addar a yayin farmakin da ta kai a kansu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Imo, Kwara - Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan yan ta'adda a jihohin Imo da Kwara.

Farmakin na cikin kokarin da sojojin Najeriya ke yi domin yaki da ta'addanci da tayar da kayar baya.

Sojojiin Najeriya
Sojoji sun yi nasara kan yan ta'adda a jihohi. Hoto: HQ Nigerian Army Asali: Getty Images

Legit gano haka ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kama yan ta'adda a Imo

Sojin Najeriya sun kai farmaki kan ƴan ta'addar IPOB a karamar hukumar Orlu a jihar Imo inda suka kama wasu daga cikin manyan yan kungiyar.

Daga cikin wadanda aka kama akwai Izuchukwu Emejuru, Chibozor Chikwe tare da kwato bindigogin zamani da na gargajiya a tattare da su.

Sojoji sun kama yan ta'adda a Onuimo

Haka zalika, rundunar sojin ta kai samame a karamar hukumar Onuimo a jihar ta Imo inda ta kama wani dan kungiyar IPOB da ake kira da Bam Bam.

Rundunar ta kuma kai wani farmaki kan yan ta'addar IPOB a karamar hukumar Okigwe a jihar Imo inda ta fatattakesu tare da kwato makamai.

'Dan ta'adda ya fada hannun sojoji a Kwara

A wani farmaki da rundunar sojin Najeriya ta kai ƙaramar hukumar Edu a Kwara, ta kama wani dan bindiga mai suna Ibrahim Abdullahi.

Ana zargin Ibrahim Abdullahi da ayyukan ta'addanci a jihar kuma an kwato bindigogi da sauran makamai a hannunsa.

Jirgin soji ya fadi a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa Jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya ya yi hatsari a wani ƙauye da ke karkashin Igabi a jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa cike da gwanancewa tare da kiyaye dokar saukar gaggawa, matuƙin jirgin ya sauka tare da tsira da ransa a hadarin.

Asali: Legit.ng

People are also reading