Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Jihohi, Sun Kama Manyan 'Yan Ta’adda
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Imo, Kwara - Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan yan ta'adda a jihohin Imo da Kwara.
Farmakin na cikin kokarin da sojojin Najeriya ke yi domin yaki da ta'addanci da tayar da kayar baya.
Legit gano haka ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojin Najeriya sun kai farmaki kan ƴan ta'addar IPOB a karamar hukumar Orlu a jihar Imo inda suka kama wasu daga cikin manyan yan kungiyar.
Daga cikin wadanda aka kama akwai Izuchukwu Emejuru, Chibozor Chikwe tare da kwato bindigogin zamani da na gargajiya a tattare da su.
Haka zalika, rundunar sojin ta kai samame a karamar hukumar Onuimo a jihar ta Imo inda ta kama wani dan kungiyar IPOB da ake kira da Bam Bam.
Rundunar ta kuma kai wani farmaki kan yan ta'addar IPOB a karamar hukumar Okigwe a jihar Imo inda ta fatattakesu tare da kwato makamai.
A wani farmaki da rundunar sojin Najeriya ta kai ƙaramar hukumar Edu a Kwara, ta kama wani dan bindiga mai suna Ibrahim Abdullahi.
Ana zargin Ibrahim Abdullahi da ayyukan ta'addanci a jihar kuma an kwato bindigogi da sauran makamai a hannunsa.
A wani rahoton, kun ji cewa Jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya ya yi hatsari a wani ƙauye da ke karkashin Igabi a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa cike da gwanancewa tare da kiyaye dokar saukar gaggawa, matuƙin jirgin ya sauka tare da tsira da ransa a hadarin.
Asali: Legit.ng