Gwamnatin Jihar Gombe Ta Yi Alkawarin Magance Matsalar Ruwa Cikin Gaggawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Gwamnan Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi alkawarin magance matsalar ruwan sha a fadin garin cikin gaggawa.
Gwamnan ya yi bayanin ne biyo bayan karuwa da matsalar ruwan sha ta yi a kwaryar jihar Gombe.
Mai taimakawa gwmantin jihar a harkokin sadarwa Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnan ya damu matuka da halin da al'umma ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa gwamna Inuwa Yahaya ya ce za a kawo karshen matsalar ruwan ne zuwa gobe Laraba, 1 ga watan Mayu.
Saboda haka ne ma ya umurci ma'aikatar samar da ruwan sha ta jihar da ta gaggauta daukan dukkan matakan da suka dace domin magance matsalar.
Gwamnatin ta koka a kan cewa matsalar ruwan ta faru ne sakamakon katsewar wutar lantarki bayan lalata layukan wuta a tsakanin Jos da Gombe.
Sun kara da cewa bayan an samu nasarar canja layi zuwa Bauchi sai iska mai karfi ta lalata wasu layukan wutan kuma.
A cewarsu hakan ne ya jawo ayyukan samar da ruwa daga Dadinkowa suka tsaya cak a fadin jihar.
Gwamnatin ta bada hakuri tare da yabawa al'ummar jihar bisa nuna juriya da suka nuna a cikin halin da suka samu kansu a ciki
A wani rahoton kuma, kun ji cewa matsalar ruwa ta yi katutu a mafi yawan garuruwan Arewacin Najeriya ciki harda Gombe, Kano, Yobe da Adamawa.
Matsalar ta jefa al'umma da dama cikin damuwa har ta fara kai wa da rashin samun gabatar da ibada cikin sauki.
Asali: Legit.ng