'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Jihar Taraba, Sun Hallaka Mutum 11
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Ƴan bindiga sun kashe mutum goma sha ɗaya tare da ƙona gidaje da dukiyoyi a ƙauyukan jihar Taraba.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyukan ƙaramar hukumar Wukari da ke kan iyakar jihohin Taraba da Benue.
Ƙauyukan sun haɗa da Apiirgwa da Deke dake gundumar Kente a Kudancin ƙaramar hukumar Wukari ta jihar Taraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shugaban al’ummar garin Adeke, Tsavyaa Adeke, ya shaida wa jaridar Leadership cewa, maharan sun mamaye garin Apiirgwa da sanyin safiyar Asabar.
Ya ce sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe a lokacin da mutane suke barci inda suka fara harbe-harbe.
"Mutane sun gudu domin tsira da rayukansu bayan sun ji ƙarar harbin bindigu, amma an kashe mutum takwas yayin da wasu suka samu raunukan bindiga."
- Tsavyaa Adeke
Shugaban ƙungiyar Tiv ta ƙaramar hukumar Wukari, Mista Aondowase Tarorshi ya ce an kashe mutum takwas a ƙauyen Apiirgwa, biyu a Tse-Deke, yayin da aka kashe mutum ɗaya a Tarorshi kan hanyar Wukari Rafinka.
Lokacin da aka tuntuɓi shugaban ƙaramar hukumar Wukari, Dauda Samaila, kan lamarin bai ɗauki kiran da aka yi masa ta waya ba.
Legit Hausa ta tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, DSP Gambo Kwache, domin samun ƙarin bayani kan harin.
Sai dai, DSP Gambo Kwache ya bayyana cewa yana hutu ne sakamakon rashin lafiyar da yake yi, amma zai ba da lambar mataimakiyarsa a kira domin samun ƙarin bayani.
Sai, dai bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun kashe wasu mutum uku da ake zargin ƴan bindiga ne.
Ƴan sandan sun kuma kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar.
Asali: Legit.ng