Home Back

'Ƴan Bindiga Sun Tafka Ɓarna, Sun Kashe Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Zamfara

legit.ng 2024/5/17
  • Yan bindiga sun harbe sakataren jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe, Musa Ille, har lahira a jihar Zamfara ranar Litinin da daddare
  • Shugaban jam'iyyar PDP na Tsafe, Garba Garewa, ne ya tabbatar da haka ranar Talata, ya ce maharan sun harbe shi a ƙofar gidansa
  • Wani mazaunin garin Tsafe ya bayyana cewa ƴan bindigan sun yaudari sakataren PDP da cewa ya fito ya duba wani abu, nan take suka kashe shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kashe Musa Ille, sakataren Peoples Democratic Party (PDP) a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Maharan sun kashe babban jigon PDP kuma sakatare a ƙofar gidansa lokacin da suka kai masa farmaki ranar Litinin da daddare.

Gwamna Dauda Lawal na PDP.
Sakataren PDP na Tsafe a Zamfara ya rasa ransa a hannun ƴan bindiga Hoto: Dauda Lawal Asali: Twitter

Shugaban jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe, Garba Garewa, shi ne ya tabbatar da kisan sakataren ga Channels tv ranar Talata, 16 ga watan Aprilu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna zargin wadanda suka kashe shi 'yan bindigan daji ne, sun shiga gidansa jiya (Litinin) suka harbe shi har lahira," in ji Garewa.

Wani mazaunin yankin, Abubakar Tsafe, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa a lokacin da ‘yan bindigar suka shiga unguwar, sai suka kira sakataren ya zo ya duba wani abu a bayan gidansa.

A cewarsa, Musa Ille ya fito waje domin duba kamar yadda suka nema ba tare da sanin su ‘yan fashi daji ba ne dauke da mugayen makamai.

Har kawo yanzu da mune haɗa muku wannan rahoton rundunar ƴan sanda ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan wannan lamarin ba.

Ku saurari ƙarin bayani...

Asali: Legit.ng

People are also reading