Home Back

"Tuggun Siyasa": Zanga Zangar Lumana Ta Ɓarke a Bauchi Kan Tsige Shugaban Ƙaramar Hukuma

legit.ng 2024/6/29
  • Kwanaki biyu bayan da gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Alkaleri, matasa sun yi zanga-zanga
  • An ruwaito cewa matasan sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna adawa da tsige Hon. Bala Ibrahim Mahmud da mataimakinsa
  • Jagoran matasan, wanda ya zanta da Legit Hausa ya aika muhimmiyar bukata ga gwamnan jihar, Bala Mohammed kan lamarin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Bauchi -Matasa daga karamar hukumar Alkaleri da ke a jihar Bauchi, sun gudanar da zanga-zangar lumana kan tsige shugaban karamar hukumar su da gwamnatin jihar ta yi.

An yi zanga-zanga a Bauchi
Bauchi: Matasa sun nemi gwamna ya dawo da ciyaman da ya sauke. Hoto: @SenBalaMohammed/X, Fantyz Guy/FB Asali: UGC

Gwamnatin Bauchi ta tsige ciyaman

A baya mun ruwaito cewa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya amince da tsige Hon. Bala Ibrahim Mahmud daga mukaminsa na kantoman Alkaleri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Mohammed, in da ta bayyana korar ta shafi mataimakin Hon. Mahmud.

Gwamnatin jihar ba ta bayar da wani dalili na dakatar da kantoman rikon da mataimakinsa ba, amma an nemi su gaggauta mika harkokin mulki tare da barin ofis.

Matasa sun yi zanga-zanga a Bauchi

Biyo bayan wannan mataki ne matasan karamar hukumar, karkashin kungiyar, KYAF Alkaleri sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da tsige Hon. Mahmud.

A zantawarsa da Legit Hausa, shugaban kungiyar wanda ya jagoranci zanga-zangar, Yusuf Sulaiman Bala (Fantyz Guy) ya roki gwamnatin jihar da ta sake duba wannan mataki.

Fantyz Guy ya ce tun da ake yin ciyamomi a yankin, ba a taba samun wanda ke kamanta adalci kamar Hon. Mahmud ba, abin da ya sa suke bakin ciki da tafiyarsa.

Ya ce idan har suka zura idanu ba tare da sun yi kira ga gwamnatin jihar ba, to haka yankin zai ci gaba da zama ba tare da wani ci gaba ba.

An nemi gwamnatin Bauchi ta kafa kwamiti

Shugaban kungiyar na KYAF Alkaleri ya ce:

"A kaf garin Alkaleri, babu wanda ke farin ciki da sauke wannan bawan Allah, domin shi ne ya nuna yana son talaka, kuma yana jan mutane a jiki.
"Gwamnatin Bala Mohammed ta mu ce, don haka muna rokon mai girma gwamna ya kafa kwamiti domin bincikar zargin da ake yi masa, hakan ne zai nuna adalcin gwamnan.
"Lokacin da za mu rika nuna tsoro ya kare, dole mu fito mu nunawa gwamnati Hon. Mahmud mutumin kirki ne, kuma taɓa shi tamkar an taɓa Alkaleri ne."

"Akwai sa hannun 'yan uba" - Chali

Shi ma da ya ke jawabi yayin zanga-zangar, Dahiru Chali, ya yi kira ga al'umar karamar hukumar Alkaleri da su kwantar da hankali kan wannan abin da ya faru.

Bello Danladi ya yi nuni da cewa tsige shugaban karamar hukumar ba zai rasa nasaba da makircin magauta ba amma suna kira ga gwamnan jihar ya yi adalci.

Kwamared Umar Abubakar Sanata, wani matashi daga masu zanga-zangar ya ce tsige Hon. Bala Ibrahim Mahmud abin baƙin ciki ne kasancewarsa mai son talakawa.

An gabatar da kudurin kirkirar jiha

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta gabatar da kuduri da ke neman a kirkiri sabuwar jiha a yankin Kudu maso Gabas.

A yayin zaman majalisar na ranar Alhamis da ta gabata, akalla 'yan majalisu 16 daga yankin ne suka gabatar da kudurin, wanda kuma ya tsallake karatu na daya.

Asali: Legit.ng

People are also reading