Home Back

Ana Tsaka da Rigimar Sarauta, Sanusi II Ya Yi Biris da Kotu, Ya Tura Wakili Nassarawa

legit.ng 2024/10/4
  • Ana tsaka da dambarwar sarautar jihar Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi sabon nadin wakilinsa a Nassarawa
  • Sanusi II ya amince da tura Abdullahi Sarki (Jakadan Garko) domin ya zama wakilinsa a karamar hukumar Nassarawa
  • Abdullahi Sarki zai ci gaba da rike mukamin kafin Sarkin ya tura hikimi da zai jagoranci karamar hukumar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Duk da rigimar sarautar Kano da ake ciki, Muhammadu Sanusi II ya sake nadin mukami a jihar.

Sarkin Kano, Sanusi II ya amince da tura Abdullahi Sarki (Jakadan Garko) domin rike karamar hukumar Nassarawa.

Wannan na kunshe a cikin wata wallafawa da Kano Emirate Council ta yi a shafinta na X a daren jiya Litinin 24 ga watan Yunin 2024.

Sanusi II ya nada Jakadan Garko wanda zai jagoranci karamar hukumar Nassarawa kafin ya tura sabon hakimi daga baya.

Jakadan Garko zai jagoranci karamar hukumar Nassarawa ne a matsayin wakilin Sarki na wani lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nadin Abdullahi Sarki na zuwa ne yayin ake ci gaba da dambarwa kan ainihin sahihin Sarki a jihar bayan hukuncin kotu.

Hukuncin kotun ya jawo rudani inda wasu ke ganin akwai rikitarwa a cikin hukuncin Babbar Kotun Tarayya.

Sai dai wasu lauyoyi sun tabbatar da cewa komai a fayyace ya ke kan hukuncin kotun babu matsala da rikitarwa a ciki.

Sheikh Dokoro ya magantu kan sarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya magantu kan rigimar sarautar Kano da ake ciki yanzu.

Shehin malamin ya shawarci Abba Kabir da Sanusi II da kuma Aminu Ado Bayero su tabbatar domin Allah suke wannan rigima.

Malamin ya ce idan har domin daukar fansa ko gabar siyasa suke yi to tabbas Allah zai wargaza su cikin sauki.

Asali: Legit.ng

People are also reading