Home Back

Sarkin Musulmi a Shirye Yake, Zai Karɓi Kowacce Dokar Gwamnatin Sokoto

legit.ng 2 days ago
  • Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, sarkin Musulmin Najeriya, yace zai yi biyayya ga gwamnatin Sokoto
  • Ya sanar da cewa zai bi duk wata doka tare da karɓarta a yayin kammala taron jin ra'ayin jama'a da aka yi
  • Antoni Janar na jihar Sokoto yace gwamnan jihar ne ke da wuƙa da nama wurin naɗin sarauta da bada aiki a masarautar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana shirinsa da burinsa na karɓar kowacce doka da gwamnatin jihar Sokoto ta gindaya.

Basaraken kuma jagoran Musulmin Najeriya, ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata a ƙaramin zauren majalisar jihar Sokoto yayin kammala jin ta bakin jama'a kan gyaran dokar 2019.

Sarkin Musulmi yace zai bi kowacce dokar gwamnatin Sokoto
Sarkin Musulmi a Shirye Yake, Zai Karɓi Kowacce Dokar Gwamnatin Sokoto. Hoto daga Sokoto Gov't Asali: Facebook

Dakta Jabbi Kilgori, ɗan majalisar masarautar kuma mai naɗa sarakuna ne ya wakilci mai martabar, rahoton Vanguard ya bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan dokar ta tsallake, za a tuɓewa Sarkin Musulmin duk wani ƙarfin ikonsa na naɗi ko tuɓe kowanne basaraken gargagjiya a jihar, jaridar The Nation ta bayyana.

Antoni janar na Sokoto yayi bayani

Kamar yadda Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, Nasiru Mohammed Binji ya bayyana, ikon naɗa hakimai, dagatai da suk wani mutum don yayi aiki da masarautar gargajiyar yana wurin masu mulki bisa la'akari da sashi na 5, ƙaramin sashi na 2 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.

Haka kundin tsarin mulki yace - Binji

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ya ce yayin aiki da tanadin kundin tsarin mulkin wanda ya bayyana ƙarara cewa naɗa hakimai ko dagatai yana wurin masu mulki, Gwamna ne mutum ɗaya da ke da wannan ikon a jihar.

Binji ya bayyana cewa, sabuwar dokar idan aka yi mata kwaskwarima za ta inganta lamurran ƙaramar hukuma da masarautu.

Gaskiyar rikicin Sarkin Musulmi da Gwamna

A wani labari na daban, fadar sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad III ta musanta ɓaraka tsakaninta da gwamnatin jihar Sokoto.

Fadar ta sanar da cewa, ita mai biyayya ce duk wata doka da gwamnatin jihar zata saka ba tare da ta bijire ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading