Home Back

Tsadar Rayuwa: Yadda Lamarin Ke Rincabe Wa Almajira Da Mabarata

leadership.ng 2024/4/28
Tsadar Rayuwa: Yadda Lamarin Ke Rincabe Wa Almajira Da Mabarata

Duk wanda ya kwana ya tashi a wannan kasa, yana cike da sanin yadda tsadar rayuwa ke ci gaba da ta’azzara, musamman a bangaren da ya shafi kayan abinci da sauran kayan masarufi.

A kullum ta Allah, idan magidanci ya je kasuwa; sai ya yi kamar ya sa hannu a ka ya ce wayyo Allah, sakamakon farashin yau daban na gobe daban.

Yana da matukar wuya a cikin irin wannan hali da ake ciki a samu magidancin da ya ke iya dora tukunya a gidansa sau uku a rana, ko da kuwa an samu damar dora tukunyar, watakila sau biyu ne ko sau daya.

Akwai magidanta da dama da suke sanya wa almajirai kwano a gidajensu, a ba su abinci da safe da rana da kuma dare, amma wannan hali da aka tsinci kai a ciki; ya dagula al’amura baki-daya.

Domin kuwa a yanzu, kusan kowa takansa ya ke yi, an koma halin nafsi-nafsi; wanda ko shakka babu Almajirai masu Allah ya ba ku mu samu, suna matukar dandana kudarsu.

Al’amarin da ya sa Almajiran suka gane cewa, lallai yanzu fa al’amuran sun canza, wannan kuma ya fara ne tun daga 29 ga Mayun 2023, bayan da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin mai, ba tare da wani bata lokaci ba farashin kaya ya fara tashi, tun ana ganin abin kamar wasa, har aka kawo wannan hali da ake ciki yanzu, domin kuwa kullum farashin kara tashin gwauron zabo ya ke yi.

Shi yasa Almajirai abin ya yi musu matukar wuya, su ma suke ji a jikinsu; musamman wadanda a da idan an ba su sadakar abincin da bai yi musu ba, kamar tuwo da sauransu sai su samu gefen kwata su zubar.

Guda daga cikin ire-iren wadannan Almajirai da abokansa suke tuna masa da irin wulakancin da suka rika yi wa tuwo a ‘yan shekarun da suka gabata, fashewa ya yi da kuka, inda su da kansu suke alakanta wulakancin da suka yi wa abincin da kuma wannan hali da suka samu kansu na rashin samun abincin akai-akai a halin yanzu a ciki.

Hausawa na fadin cewa, duk bakin da Allah ya tsaga; ba ya hana shi abinci ko da kuwa babu dadi. Wannan magana ta Bahaushe, ko shakka babu; haka ta ke babu wani gyara a ciki, domin kuwa ba mutum ba ko dabbar da Allah ya halitta, ba ya hana ta abin da za ta kai baki.

Har ila yau, wannan tsadar rayuwa da ake fama da ita, ya sa wasu daga cikin jihohi; musamman a Arewa, fara yin bore ta hanyar aiwatar da zanga-zanga, domin nuna rashin amincewarsu da halin da suka tsinci kansu a ciki.

Koda-yake, a hannu guda kuma, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nuna damuwarsa tare da sanya dokar ta-baci, a kan harkokin noma; inda gwamnatinsa ta sha alwashin sama wa ‘yan Nijeriya wadataccen abinci, ta yadda har sai an samu rarar da za a rika fita da shi zuwa kasashen waje.

Haka nan, su ma gwamnoni daga jihohi daban-daban, sun yi yunkurin daukar matakai; musamman a bangaren da ya shafi kayan abinci, duk dai don rage wa al’umma radadin wannan hali da suke ciki.

A nan, muna sake yin kira ga gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi da su sake jajircewa tare da mayar da hankali a kan wadannan matsaloli da ke addabar wannan kasa tun kafin kan talakawa ya kwace, su fito su fara yin abin da ba shikenan ba.

Dalili kuwa shi ne, akwai wadanda su ke ganin cewa, duk duniya babu wanda ya kai talakan  Nijeriya hakuri da juriya, domin kuwa ya jure rashin wutar lantarki da rashin hanyoyi da matsalar lafiya da ilimi da ruwan sha da sauran makamantansu, amma ga dukkan alamu an kusa zuwa inda hakurin nasa zai tike.

Saboda haka, yanzu dai shawara ta rage ga mai shiga rijiya, ko dai gwamnati ta yi abin da ya dace, ko kuma a nan gaba ta yi kuka da kanta. Domin kuwa, duk wanda zai sha inuwar gemu; bai kai makogwaro ba.

 
People are also reading