Home Back

Hisbah Ta Ware Wa ‘Yan Jarida Gurbin Mutane 50 A Auren Gata A Kano

leadership.ng 2024/5/17
Hizba Ta Gana Da Kungiyar Masu Bege, Ta Bukaci Su Tsabtace Harshe

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da ware wa ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai gurbin mutane 50 a auren gata da za a sake yi a jihar.

Daurawa ya ce shirin na da nufin karfafa alaka a tsakanin ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Sheikh Daurawa ya bayyana nasarar da hukumar ta yi a baya, na aurar da mutane 1,800.

Hakan ne ya sa shugaban na Hisbah ya ce hukumar ta yanke shawarar fadada shirin zuwa fannoni daban-daban kamar aikin jarida, doka, da kiwon lafiya.

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa, an shirya bikin auren da nufin inganta kyawawan dabi’u a cikin al’umma da kuma rage lalata a tsakanin matasa maza da mata.

Baya ga fadada shirin auran gatan, Sheikh Daurawa ya bayyana kafa makarantar Hisbah tare da hadin gwiwar makarantu a Kano da suka hada da Jami’ar Yusuf Maitama Sule (Yumsuk), Kwalejin Aminu Kano, Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi, da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Ya ce makarantar za ta ke bayar da horo kan aikin Hisbah, tare da bayar da takardar shaidar kammala karatu.

“Kwalejin Hisbah na da burin bai wa dalibai ilimi da makamar aiki game da ayyukan Hisbah, domin yada manufar hukumar na wanzar da zaman lafiya a Jihar Kano.”

Sai dai Daurawa bai sanar da ranar da za a fara shirin kashi na biyu na auren gatan ba.

People are also reading