Home Back

‘Yansanda Sun Kama Matashi Kan Daba Wa ‘Yar Talla Wuka A Yobe

leadership.ng 2024/5/17
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

Rundunar ‘yansandan Jihar Yobe, ta kama wani matashi mai suna Sani Musa mai shekaru 22, wanda aka fi sani da Regis Oga Soja a unguwar Nawa Nawa Damaturu kan zargin daba wa wata ‘yar talla mai shekaru 24 wuka. 

Matashin ya kuma kwace wayar ‘yar tallan.

Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga watan Afrilu, 2024.

Abdulkarim, ya ce an kama Musa ne tare da wayar ‘yar tallan kirar Itel A663LC/MTN a hannunsa.

DSP Dungus ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi.

Kwamishinan ‘yan sanda, Garba Ahmed, ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da adalci ba.

CP Garba ya kuma karfafa wa jami’an rundunar gwiwa da su ci gaba da tabbatar da doka da oda a jihar Yobe.

Ya kuma yaba wa al’ummar jihar kan goyon bayan da suke ba su na yaki da aikata laifuka a jihar.

People are also reading