Home Back

Sudan: RSF za ta bude hanyar fita daga Darfur

dw.com 2024/9/27
Mayakan RSF na Sudan
Mayakan RSF na Sudan

Rundunar mayakan RSF ta ce za ta bude hanyoyin fita daga yankin El-Fasher da ke Darfur, sakamakon fadan da ya sake rincabewa a makwannin baya-bayan nan. A sakon da rundunar ta wallafa a shafinta na X da aka fi sani da Twitter a baya, ta ce za ta taimaka wa jama'a su bar yankin zuwa wasu sassan kasar tare da ba su kariya.

Karin bayani: 

RSF ta bukaci mazauna El-Fasher da su kaurace wa yankunan da ake fada da ma inda za su iya kai wa farmaki. Fiye da shekara guda kenan da Sudan ta fada cikin rikicin shugabanci tsakanin shugaban rundur sojin kasar, Abdel Fattah al-Burhan da kuma na RSF da ke karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Daglo. Rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 15,000 a cewar kwararru a Majalisar Dinkin Duniya.

People are also reading