Home Back

Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare a zirin Gaza

dw.com 2024/5/14
Sojojin Isra'ila a harabar asibitin Al Shifa da ke birnin Gaza.
Sojojin Isra'ila a harabar asibitin Al Shifa da ke birnin Gaza.

Tun daga daren jiya litinin 25 ga watan Maris 2024, zuwa wayewar gari Isra'ila ta yi ta kai hare-hare babu kakkautawa a yankin da kimanin mutane sama da milyan daya suka nemi mafaka a shiyyar asibitin Al Shifa.

Karin bayani: Bin Salman ya bukaci tsagaita wuta a Gaza

A yankin arewacin Gaza, guda daga cikin iyalan Hassera ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa sojojin Isra'ila sun shafe kusan dukkan zuri'arsu daga doron kasa tare da kashe dubban mutane a yankin na asibitin Al-Shifa.

Sabbin hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya cimma matsayar bai daya a karon farko na bukatar gaggauta tsagaita bude wuta a zirin Gaza, kudurin da Amurka ta ki kada kuri'a kan gaza amincewa da daftarin da ta gabatar kan bukatar tsagaita wutan.

Ma'aikatan lafiyar Gaza ta sanar da sabbin alkaluman Falasdinawan da suka mutu a yakin na Gaza da adadinsu ya zarta dubu 32,414 galibinsu mata da kananan yara.

People are also reading