Home Back

Abubuwan Da Za A Rika Tuna Saratu Gidado Da Su A Fagen Fim

leadership.ng 2024/5/14
Abubuwan Da Za A Rika Tuna Saratu Gidado Da Su A Fagen Fim

Labarin rasuwar marigayiya Saratu Gidado da ta yi suna a fagen fina-finan Hausa (Kannywood) har ma da wasu na turanci da take yi jefi-jefi, ya yi matukar girgiza ba kawai fage.

Fim ba har da sauran al’umma bisa yadda jarumar ta shahara da kuma irin jin kan da ta fara yi ga al’umma ta gidauniyarta.

Ita dai Saratu Gidado wacce ta rasu ranar Talata 9 ga Afrilun 2024, an haife ta ce a Jihar Gombe, a ranar 17-01-1968. Sannan ta yi karatu tun daga matakin firamare a jihar Kano. Daso, wadda tayi suna wajen fitowa a matsayin “Ba Sani Ba Sabo” a shirye shiryenta, ta kasance abar so a wajen masu kallo saboda yadda take yin abu da gaske kuma babu tsoro a cikin Shirin Fim.

Daso ta yi suna ne musamman wajen fitowa a matsayin mara tsoro, masifaffiya, da kuma ba sani ba sabo. Wannan shi ne ya sa ta fita daban a cikin ragowar jarumai mata a masana’antar saboda tana iya fitowa a duk yanayin da ake bukata ta fito musamman a matsayin uwa mai tsoratarwa.

Marigayiyar dai ta kasance sananniya a idon duk wani wanda yake Kallon fina-finan Hausa da ma wanda ba ya kallo saboda irin rawar da take takawa sannan kuma ta kasance mace tilo a masana’antar da idan ana bukatar salo na fitowa a uwa ko mace mara kirki ko mara tsoro ko mara tausayi ita ce kadai za ta iya fitowa ta bayar da abinda ake bukata.

Har ila yau, ta kasance abar soyuwa a zukatan masu kallo saboda duk da irin ba sani ba sabo da take nunawa amma tana da faran-faran da mutane domin an yi mata shaidar cewa mutuniyar kirki ce.

A shekara ta 2000 ta tsunduma harkokin fina finan hausa, inda ta fara fitowa a cikin Shirin “Linzami Da Wuta” wanda kamfanin Sarauniya ya shirya. Wasu daga cikin fina-finan da ta fito sun hada da ‘Yar Mai Ganye da Nagari da Sansani da Mashi da Fil’azal da Jakar Magori da Gidan Iko da Gidauniya da Uwar Kudi da Gani Ga Ka da kuma Shirin turanci na “There is Way” da kamfanin Jammaje ya shirya.

Shiri na kwana kwanan nan da ya sake fitowa da ita shi ne Shirin LABARINA na kamfanin Saira Mobies, domin an yaba irin rawar da ta taka kuma. A shekara ta 2016 ne Sarkin Kano na 14 Muhammad Sanusi II ya nada ta a matsayin Jakadiya.

Ta kasance mai son taimakawa marayu wajen samar musu abinci da kayan sakawa sannan tana yawan bayyana a shafukan sada zumunta inda take bayyana ra’ayinta a kan abubuwan da ake tattaunawa sannan kuma tana da wata gidauniya ta tallafawa marasa galihu inda ko a cikin watan Ramadana da ya wuce ta rarraba kayan abinci ga marayu da mabukata.

Masu sharhi a kan harkokin fina-finan Hausa dai sun bayyana irin rawar da Daso take takawa a matsayin ta musamman saboda har kawo yanzu babu wata mace da ta taso wadda ake ganin za ta iya maye gurbinta kuma hakan ne ya sa dole idan ana bukatar salo irin nata ita kadai ake iya nema.

Kamar yadda iyalai da ‘yan uwanta suka bayyana, ta rasu da safiyar Talata 9-04-2024  bayan ta dauki azumi na 30, kuma tuni aka yi mata sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

People are also reading