Home Back

SHAYE-SHAYE: An kama wasu matasa maza da mata 60 a wani gida a Abuja da ke bukin gwanin barankaɗewa

premiumtimesng.com 3 days ago
SHAYE-SHAYE: An kama wasu matasa maza da mata 60 a wani gida a Abuja da ke bukin gwanin barankaɗewa

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, a ranar Lahadi, ta kai samame wani gida da matasa suke dabdalewar shaye-shayen kwayoyi da ganye inda ta kama mutane 60.

Kakakin hukumar Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kaiwa matasan samame bayan sun samu bayanan sirri game da wannan dabdalewa da suka shirya yi.

An kama mata 35 da wasu maza 25 maske sun rankwale da kwayoyi, suna bushe-bushe naɗaɗɗun mandula na wiwi da wasu kwayoyi.

Wasunsu an sake su bayan sun biya tara wasu kuma suna tsare hannun ƴan sanda.

Matasan dai suna bukin nuna wanda ya iya dakewa ne bayan ya yi matuƙar maskewa, ya haɗiyi kwayoyi batare da ya nuna gazawa ba.

An kama su a wani gida dake rukunin gidaje na Sun City dake Abuja.

A cikin matasan da aka kama an samu wasu mutum shida da ke ɗauke da wasu sunadarai na musamman na rankwalewa, waɗanda aka kama sun haɗa da Victoria Adoga, Hamza Yari, Joanne Essein, Socchima Valentine Jago Imole da Charles Indobuibisi.

People are also reading