Home Back

GARGAƊIN TINUBU GA TSAGERUN KUDU DA NA AREWA: ‘Za mu tarwatsa duk mai neman tarwatsa Najeriya’

premiumtimesng.com 2024/5/14
GARGAƊIN TINUBU GA TSAGERUN KUDU DA NA AREWA: ‘Za mu tarwatsa duk mai neman tarwatsa Najeriya’

Shugaba Bola Tinubu ya yi kakkausan gargaɗin cewa gwamnatin sa za ta yi maganin duk wani tsagera ko tsagerun da ke neman tarwatsa Najeriya, ko a ina yake.

Tinubu ya yi wannan gargaɗin a ranar Laraba, lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugabannin Kungiyar Kare Muradun Yarabawa Zalla, wato Afenifere, a Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja.

Ya ce gwamnatin sa na kan hanyar shata nagartaccen tanadin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, ta hanyar Inganta tsaro, yayin da a gefe guda kuma gwamnatin na ci gaba da kawar da manyan ƙalubalen da suka yi wa ƙasar nan kaka-gida.

Tinubu ya ce gwamnatin sa ta dukufa wajen bunƙasa ƙarfin ikon samun sukunin ƙarfin iya sayen kayan abinci, masarufi da biyan buƙatun kowane ɗan Najeriya.

Ya ƙara da cewa tilas sai Najeriya ta tsare tare da gina tattalin arzikin ta bisa nagartaccen tushe da tibali, kafin ta cimma nasarorin da ta ke son cimmawa a wasu fannoni daban-daban.

“Babban makamin yaƙi da fatara da talauci shi ne inganta fannin ilmi. Idan muna son ƙarfafa al’umma, to kuwa tilas sai an ƙarfafa matasa sosai da sosai.

“Saboda mun ga yadda iyaye ke gaganiyar ɗaukar ɗawainiyar karatun yaran su. Dalili kenan muka fito da Shirin Lamunin Ɗalibai a ƙarƙashin sabuwar Hukumar NELFUND.”

Tinubu ya ƙara da cewa kuma tuni gwamnatin sa ta fara tsara yadda za ta shawo kan gagarimar matsalar rashin aikin yi.

“Tilas mu taimaka wa marasa galihu domin su samu tagomashi a cikin al’umma. Kuma muna tunanin yadda za a fara biyan alawus-alawus ga marasa aikin yi, maimakon zaman-kashe-wando.”

Da ya koma kan matsalar tsaro, Tinubu ya ce “za mu tarwatsa duk wasu maso hanƙoron tarwatsa Najeriya.”

Tinubu ya yi wannan kakkausan kalami mako ɗaya bayan damƙe wasu tsagerun da ke hanƙoron neman tarwatsa Najeriya.”

Shugabannin Afenifere sun ce su na goyon bayan gwamnatin Tinubu, ko ana ha-maza-ha-mata.

Mamba a cikin tawagar dattawan na Afenifere, Olu Falae, ya jinjina wa Shugaba Tinubu, tare da alwashin ci gaba da ba shi goyon baya a a halin ƙaƙa.

People are also reading