Home Back

EFCC: An Samu Matsala a Shirin Gurfanar da Tsohon Gwamna Kan Badaƙalar N80bn

legit.ng 2024/7/3
  • Kotu ta sauya ranar gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello daga yau Alhamis 13 zuwa 27 ga watan Yunin 2024
  • Hakan ya faru ne sakamakon buƙatar da lauyoyin EFCC suka nema na ɗage ranar saboda rashin isasshen lokacin zuwa kotu
  • Lauyan Yahaya Bello, Adeola Adedipe, SAN ya ce ya yi mamakin yadda lauyan EFCC ya halarci zaman kotu yau Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya ta sauya ranar da za a gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan tuhumar satar maƙudan kuɗi da suka kai N80bn.

Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin masa zagon ƙasa (EFCC) ce ta zama silar sauya ranar daga 13 ga watan Yuni zuwa 27 ga watan Yunin 2024.

Yahaya Bello.
An ɗaga ranar da za a gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu Hoto: Alhaji Yahaya Bello Asali: Twitter

Kamar yadda The Nation ta kawo a rahoto, EFCC ta janye buƙatar ɗage ranar gurfanar da Yahaya Bello ba tare da hukumar da sanar da lauyoyin tsohon gwamnan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon haka aka sake zaɓar ranar 27 ga watan Yuni domin kawo Yahaya Bello gaban kotun kan tuhume-tuhume halasta kuɗin haram wanda EFCC ta shigar.

An cimma wannan matsaya ne yayin zaman kotun na yau Alhamis, 13 ga watan Yuni, 2023.

A zaman ɗaya daga cikin lauyoyin Yahaya Bello, Adeola Adedipe, SAN, ya shaidawa kotu cewa lauyoyin EFCC sun same su sun ce ranar 13 ga Yuni ba ta masu ba.

Ya ce lauyoyin hukumar yaƙi da rashawar sun faɗawa Aliyu AbdulWahab, SAN, ɗaya daga cikin lauyoyin wanda ake ƙara cewa suna son canaja ranar zaman kotu.

Sakamakon haka lauyoyin tsohon gwamnan Kogi suka amince a canja ranar zuwa lokacin da ya dace kuma masu ƙara ke da sarari.

Ya ce ya yi mamaki da ya samu labarin cewa lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya halarci zaman kotu duk da rokon da suka yi na sauya ranar zaman.

A rahoton kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom ya koma jami'ar Uyo (UNIUYO) domin ya ƙarisa karaun digirinsa na uku (PhD)

Fasto Umo Eno ya gabatar da babi na 1, 2 da na 3 a kundin aikin binciken da zai yi a gaban kwamitin malaman jami'ar.

Asali: Legit.ng

People are also reading