Home Back

Isra’ila Ta Lashi Takobin Rama Harin Da Iran Ta Kai Mata

leadership.ng 2024/5/2
Isra’ila Ta Lashi Takobin Rama Harin Da Iran Ta Kai Mata

Isra’ila ta sha alwashin mayar da martani kan Iran, bayan harin ramuwar gayyar da ta kai mata a ranar Asabar. 

Sai dai ba ta bayyana lokaci da kuma girman irin matakin ramuwar da za ta dauka ba.

Babban hafsan sojin Isra’ila Herzi Halevi, ne ya shaida wa dakarun sojin kasar hakan yana mai cewa babu gudu ba ja baya sai an mayar da martani ga harin da Iran ta kai kan kasar.

Sai dai Iran ta mayar da martanin cewa ba ta da burin ganin varkewar yaki tsakaninta da Isa’ila, amma fa duk kasar da ta lakuci hancinta da za ta dandana kudarta.

A can Zirin Gaza kuwa, a ranar Litinin likitoci suka sake gano wani makeken kabari a Al-Shifa asibiti mafi girma a yankin na Gaza, wanda sojojin Isra’ila suka shafe mako biyu suna yi wa kawanya gami kai samame cikinsa.

Yanzu haka dai likitocin sun tabbatar da gano gawarwakin mutum 10 a cikin makeken kabarin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wani wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa kimanin kashi 90 cikin 100 na gine-gine kusan 4,000 da ke kan iyakar yankin gabashin Gaza, Isra’ila ta ruguza yayin hare-haren da take kai wa da sunan murkushe mayakan Hamas.

People are also reading