Home Back

NOMA TUSHEN ARZIKI: Gwamna Yusuf ya yaba wa Tinubu kan gudummawar takin zamani lodin mota 70 da ya ba manoman Kano

premiumtimesng.com 2024/6/28
NOMA TUSHEN ARZIKI: Gwamna Yusuf ya yaba wa Tinubu kan gudummawar takin zamani lodin mota 70 da ya ba manoman Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir-Yusif ya yi godiya tare da jinjina ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, dangane da gudummawar takin zamani da ya ba manoman Jihar Kano, har lodin mota 70.

Shugaba Tinubu ya bayar da takin zamanin domin bunƙasa harkokin noma a Jihar Kano.

Wannan godiyar na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature ya fitar a ranar Alhamis.

Gwamna Abba ya bayyana haka lokacin da ya ke ƙaddamar da ayyukan titina a Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, inda ya ce Shugaba Tinubu ya bayar da gudummawar takin zamanin har cikin mota 70.

Ya ce Tinubu ya na farin cikin ganin ya na tallafa wa manoman Jihar Kano, domin a bunƙasa harkokin noma a jihar.

Kafin nan dama Gwamna Abba ya umarci Hukumar KASCO ta Jihar Kano ta fara gagarimin aikin sarrafa takin zamani, domin tunkarar noman damina mai zuwa.

Kano a matsayin ta na ɗaya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen bunƙasa harkokin noma, ta na noma masara, shinkafa, wajen soja, riɗi, gyaɗa, soɓorodo da dawa.

People are also reading