Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Dalilin Sake Neman Ciyo Bashin Dala 2.5bn

legit.ng 2024/6/29
  • Gwamnatin tarayya ta fito ta kare matakin da ta ɗauka na neman sake ciyo bashin Dala 2.5bn daga wajen bankin duniya
  • Ministan kasafin kuɗi, Sanata Atiku Bagudu, ya bayyana cewa gwamnati ba ta da isassun kuɗaɗen da za ta aiwatar da wasu ayyukan da ke kasafin kuɗin shekarar 2024
  • Ministan ya yi bayanin cewa za a ciyo bashin ne domin gudanar da wasu muhimman ayyuka guda huɗu a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta yi magana kan dalilinta na neman sake ciyo bashi a wajen bankin duniya.

Ministan kasafin kuɗi, Sanata Atiku Bagudu, ya ce kasafin kuɗin shekarar 2024 da aka gabatar, za a aiwatar da wani ɓangare na shi ne da N50bn daga asusun PIDF.

Gwamnatin Tinubu za ta ciyo bashin $2.5bn
Gwamnatin tarayya za ta gudanar da muhimman ayyuka da bashin $2.5bn Hoto: @DOlusegun Asali: Twitter

Dalilin gwamnatin Tinubu na neman bashin $2.5bn

Sai dai ya yi nuni da cewa N50bn ɗin ba za ta isa ba wajen samar da ayyukan ci gaba na “Renewed Hope Transformational Projects”, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa hakan hakan ya sa gwamnatin tarayya ta nemi rancen dala biliyan 2.5 daga bankin duniya.

Bagudu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yiwa taron haɗin gwiwa na kwamitocin majalisar dattawa da na wakilai kan tsare-tsare da harkokin tattalin arziƙi na ƙasa dangane da ƙudirin ƙarin kasafin kuɗi.

Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba shugabannin bankin duniya za su yi taro domin yanke shawarar amincewa da bayar da lamunin, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Me gwamnati za ta yi da kuɗaɗen?

Ya ce gaba ɗayan kasafin kuɗin, wanda har yanzu ake tsarawa, za a ware shi ne ga wasu muhimman ayyuka guda huɗu.

Ya ce ayyukan sun hada da titin Legas zuwa Calabar, titin Sokoto zuwa Badagry da ake shirin yi, da kammala ayyukan layin dogo da kuma gyara da faɗaɗa madatsun ruwa domin bunƙasa noma.

CBN ya daina ba gwamnati bashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya sanar da daina bayar da bashin 'Ways and Means' ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Gwamnan babban bankin na CBN, Olayemi Cardoso, ya ce ya ɗauki matakin ne saboda gazawar gwamnati wajen biyan basussukan da ake bin ta.

Asali: Legit.ng

People are also reading