Home Back

Harin Masallacin Kano: Kotu Za Ta Fara Sauraron Shari’ar Matashin da Ya Kona Masallata

legit.ng 2024/7/3
  • Wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kano za ta fara sauraron shari'ar matashin da ake zargin ya bankawa masallaci wuta a Gezawa
  • Kotun ta sanya ranar 4 ga watan Yuli, domin fara sauraron shari'ar Shafi’u Abubakar kan tuhume-tuhume uku da gwamnati ke yi masa
  • An ce Shafi’u ya cinnawa masallacin wuta tare da kulle kofofinsa a ranar 15 ga watan Mayu, inda akalla mutane 19 suka mutu daga wutar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kano ta sanya ranar sauraron karar da aka shigar kan matashin da ya banka wuta a wani masallaci da ke garin Gezawa.

Kotu ta yi magana kan shari'ar harin masallacin Kano
Kotu za ta fara sauraron shari'ar harin masallacin Kano a watan Yuni. Asali: UGC

A ranar Juma'a kotun ta sanya ranar 4 ga watan Yuli, domin fara sauraron shari'ar Shafi’u Abubakar, mai shekaru 38, kan laifin kona masallata tare da ajalin mutane 19.

Ana tuhumar matashin da laifuffuka 3

Ana tuhumar Abubakar wanda ke zaune a karamar hukumar Gezawa a Kano, da aikata barna da wuta, haddasa mummunan rauni da kuma kisan kai, in ji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito laifuffukan sun ci karo da tanadin sashe na 336, 247 da 221 na dokar shari’a ta jihar Kano.

A zaman kotun na yau, Lauyan masu gabatar da kara daga ma’aikatar shari’a ta Kano, Mista Salisu Tahir ya shaida wa kotun cewa ya karbi kwafin kundin karar daga hannun ‘yan sanda.

Tahir ya ce:

"Muna neman karin wa'adi domin sake gurfanar da shi gaban kotu wanda zai ba mu damar kara yawan wadanda suka mutu daga 14 zuwa 19 da kuma karin shaidu."

Wanda ake zargi ya samu lauya

Ana zargin Shafi’u Abubakar da cinnawa masallaci wuta a kauyen Larabar Abasawa da ke Gezawa a Kano tare da kulle kofofinsa a ranar 15 ga watan Mayu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wanda ake tuhumar ya amsa laifuffkan guda uku da ake tuhumarsa da su.

NAN ta ruwaito cewa Auwal Abubakar, daga majalisar lauyoyi ta LACN ya sanar da cewa zai kare wanda ake zargin bayan kotu ta nemi majalisar ta ba lauyan da zai kare Shafi’u.

Mutane 21 sun mutu a harin masallaci

A wani labarin, mun ruwaito cewa adadin masallatan da suka rasu sakamakon harin da wani matashi ya kai masallacin da suke Sallah a garin Gezawa ya kai 21.

Wani mazaunin kauyen Larabar Abasawa inda lamarin ya faru ya bayyana cewa sun binne gawar mutum 21 yayin da wasu mutum 4 ke kwance a asibiti rai hannun Allah.

Asali: Legit.ng

People are also reading