Home Back

NELFUND ta Fadi Daliban da Su ka Cancanci Lamunin Karatu

legit.ng 2024/7/3
  • Hukumar kula da bayar da lamunin karatu ga daliban Najeriya ta bayyana cewa duk wanda ya cancanta zai samu tallafin ba tare da sa hannun uban gida ba ko an san wani ba
  • Babban daraktan hukumar a bangaren kudi da gudanarwa, Dr. Fred Akinfala ne ya bayyana haka, inda ya ce shirin na daya daga abin da za a yi alfahari da shi a kasar nan
  • NELFUND ta bayyana cewa nan gaba za ta wallafa sunayen jami'o'in da sauran manyan makarantun da su ka aika mata da sunayen dalibansu da ke neman lamunin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Hukumar da ke lura da asusun bayar da lamunin karatu na kasa (NELFUND) ta tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa za ta bawa daliban kasar nan lamunin karatu ba tare da sun bukaci uban gida ya shige masu gab aba.

Babban daraktan hukumar a bangaren kudi da gudanarwa, Dr. Fred Akinfala ne ya bayyana haka, inda ya jaddada cewa ana bin gaskiya wajen tsarin bayar da lamunin karatu ga daliban kasar nan.

Bola Tinubu
Gwamnatin tarayya ta ce ba sai da uban gida za a bayar da lamunin karatu ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Dr. Akinfala ya bayyana yakinin cewa idan shugaban Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adinsa, tsarin bayar da lamunin karatu zai zama mafi kyawun ayyukan da za a yi alfahari da shi kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

”Lamunin karatu zai habaka ilimi,” Dr. Akinfala

Babban darakta a hukumar asusun ba dalibai tallafin karatu, Dr. Fred Akinfala ya bayyana cewa tsarin lamunin karatu da gwamnatin Bola Tinubu ta dauko zai habaka ilimi a kasar nan.

Ya ce tsarin da gwamnati ta bijiro da shi zai taimakawa dalibai su kammala karatunsu ba tare da matsala ko samun tsaiko ba, wanda zai bunkasa tattalin arzikin kasa saboda karuwa masu ilimi.

A wani labari da The Guardian ta wallafa, hukumar NELFUND a sanarwar da kakakinta Nasir Ayitogo ya sanyawa hannu, ya ce za su wallafa jerin manyan makarantun da su ka aika da sunayen daliban da ke neman lamunin.

Dalibai 9000 sun nemi lamunin karatu

A wani labarin kun ji hukumar NELFUND ta bayyana cewa bayan ba dalibai damar cike bayanan neman lamunin karatu, akalla dalibai 9000 ne su ka nemi rancen daga gwamnatin tarayya.

Daraktan hukumar, Akintinde Sawyerr ya bayyana cewa akalla 90% na jami'o'in kasar nan sun aika da bayanan dalibansu domin fara tantancesu domin raba bashin karatun.

Asali: Legit.ng

People are also reading