Home Back

JAMB Ta Bayyana Adadin Daliban da Za Su Sake Zana Jarabawar UTME, an Sanya Rana

legit.ng 2024/7/5
  • Hukumar JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2024 da ta rike wa dalibai 3,921 da ta yi bincike a kan su
  • Hukumar jarabawar ta kuma sanar da cewa za ta sake gudanar da jarabawar UTME ta shekarar 2024 ga dalibai 24,535
  • Haka zalika, JAMB ta sanar da tsawaita ranar rajistar jarrabawar shiga aji biyu na jami'a (DE) a zangon karatu na 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A ranar Lahadi ne hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta ba da sanarwar fitar da sakamakon jarabawar UTME na dalibai 3,921 da ta rike.

JAMB ta yi magana kan jarabawar UTME 2024
JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar UTME 2024 na daliban da ta rike masu. Hoto: @ProfTahirMamman Asali: Twitter

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Fabian Benjamin ya fitar, JAMB ta kuma ce za ta sake gudanar da jarabawar ga dalibai 24,535.

Dalibai 24,535 za su sake zana UTME 2024

Jaridar The Punch ta ruwaito daliban za su sake zana jarabawar ne bayan da JAMB ta yi nazari yadda aka gudanar da jarrabawar a wasu cibiyoyi inda aka samu rahoton rashin bin ka'idoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Fabian Benjamin:

"Wadanda za su sake zana jarabawar za su fitar da takardun su (slip) daga ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024, domin sanin cibiyoyin da za su zana jarabawar.
"Za a gudanar da jarrabawar a ranar Asabar, 22 ga watan Yunin 2024, makwanni biyu nan gaba, wanda zai bai wa dalibai 24,535 da abin ya shafa isasshen lokaci domin yin shiri."

JAMB ta tsawaita rajistar DE

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hukumar JAMB ta kuma tsawaita ranar rajistar jarrabawar shiga aji biyu na jami'a (DE) zuwa Litinin 17 ga Yuni, 2024.

Sanarwar ta kara da cewa:

“A halin yanzu, mun fitar da sakamakon jarabawar dalibai 3,921 da muka kammala bincike a kan su. A yanzu JAMB ta saki jimillar sakamakon jarabawar dalibai 1,883,350.
"Hukumar na kira ga daliban da aka saki jarabawarsu da su duba sakamakon daga ranar Asabar, 1 ga watan Yuni 2024, ta hanyar aika RESULT zuwa 55019 ko 66019."

'Yan kwadago sun dura bankin Legas

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Legas sun kai samame wani bankin Polaris da ke Alausa inda suka fatattaki jama'ar da ke ciki.

A jihar Imo kuwa, kungiyar kwadago ta NLC ta rufe bankuna, sakatariyar jiha da ta tarayya bisa bin umarnin uwar kungiya na shiga yajin aiki.

Asali: Legit.ng

People are also reading