Home Back

An Gano Yarinya Yar Shekaru 10 da Aka Sace a Cikin Firinji a Kaduna

legit.ng 2024/5/17
  • Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta kama wani mai shago Aminu Garba da zargin ya kulle wata yarinya a cikin firinjin shagonsa
  • ASP Mansir Hassan, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Kaduna ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai
  • Ya ce fusatattun matasa ne su ka gano yarinyar bayan mai shagon ya musanta cewa ya na da masaniya kan inda yarinyar ya ke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kaduna-Jami'an yan sandan Kaduna sun tabbatar da kama wani mai shago, Aminu Garba da ake zargi da sace wata yarinya mai hekaru 10, Hanifa a jihar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Mansir Hassan ya tabbatarwa manema labarai cewa sun gano yarinya a kulle cikin firinji.

An kama mai shago da zargin sace yar shekaru 10 a Kaduna
Ana zargin Aminu Garba da rufe Hanifa mai shekaru 10 a cikin firinji Hoto:Getty images Asali: Getty Images

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa an gano yarinyar mai suna Hanifa a kulle cikin na'urar sanyaya kayan bayan wasu matasa sun bincike shagon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifiyar Hanifa ta nemi taimakon yan sanda

A cewar kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, a ranar Asabar ne mahaifiyar Hanifa, Uwaila Idris ta kai kara wurin yan sanda.

Uwar yarinyar ta shaidawa jami'an tsaro cewa ta na zargin mai shago Aminu da sace 'yar ta Hanifa.

Ta ce ta aiki Hanifa mai shekaru 10 shagon Aminu amma ba ta dawo ba, wanda hakan ya tayar ma ta da hankali matuka.

Yadda aka gano yarinyar da aka sace

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa yan sanda sun gayyaci Aminu, amma ya musanta zargin da Uwaila ke masa.

Sai dai matasan yankin sun ki amincewa da lamarin, wanda ya sanya su bincikar shagon har aka gano Hanifa a kulle cikin firinjin.

ASP Mansir Hassan ya ce su na zurfafa bincike, kuma da an kammala za a gurfanar da shi gaban kotu.

An sace wata yar shekaru 17

Mun kawo mu ku rahoton yadda wasu ma'aurata da su ka sace wata yarinya mai shekaru 17 a karamar hukumar Tudun Wada dake Nomansland a jihar Kano.

Ana zargin Mista da Miss Mathew Auta da laifin hada baki wajen sace Amira Isa Takai mai shekaru 17, sai dai ma'auratan sun musanta zargin da ake mu su.

Asali: Legit.ng

People are also reading