Home Back

Zamu Ba Wa Maraɗa Kunya A Wasanmu Na Gaba Da Ƙasar Benin – Finidi

leadership.ng 2024/7/3
Zamu Ba Wa Maraɗa Kunya A Wasanmu Na Gaba Da Ƙasar Benin – Finidi

Kocin Super Eagles Finidi George, ya bayyana cewar yana da matuƙar kwarin gwiwa dangane da ƴan wasansa, waɗanda yace zasu ba wa maraɗa kunya a wasan da Nijeriya zata baƙuncin ƙasar Benin a cigaba da wasannin neman cancantar buga kofin Duniya.

Tawagar Super Eagles wacce Finidi George yake jagoranta za ta yi tattaki har ƙasar Ethiopia domin kece raini da ƙasar Benin a babban filin wasa na Felix Boigny da ke Abidjan, wasan shi ne na huɗu a rukunin C wanda ƙasar Lesotho take jagoranta.

Finidi ya bayarda tabbacin cewar Nijeriya za ta dawo da martabarta a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 bayan da ta yi rashin nasara a wasanni uku da ta buga.

Har yanzu tawagar ta Super Eagles ba ta samu nasara ba a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, bayan da ta sake yin kunnen doki 1-1 a gida da Afirka ta Kudu ranar Juma’a a garin Uyo da ke kudancin Nijeriya.

Kasar Lesotho ce ke kan gaba a rukunin da maki biyar, maki ɗaya tsakaninta da Rwanda da Benin, yayin da Afirka ta Kudu ke matsayi na hudu, Nijeriya ta biyar sai kuma ƙasar Zimbabwe da ke matsayi na ƙarshe da maki biyu.

A watan Afrilu ne aka miƙa wa tsohon ɗan wasan na Nijeriya Finidi ragamar jagorancin tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar bayan ta sha kashi a hannun Ivory Coast a wasan ƙarshe na gasar cin kofin ƙasashen Afrika.

People are also reading